Daga Rabiu Ali Indabawa,
Rundunar ‘yan sanda reshen Jihar Oyo ta tabbatar da kisan wasu mazauna garin Idere na jihar da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka yi a ranar Asabar. ‘Yan sanda sun lura cewa an kama wasu da ake zargi da hannu a lamarin.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Oyo, Nwachukwu Enwonwu a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Ibadan a ranar Laraba, ya sake tabbatar da cewa an sace wani Likita a garin Tapa. A cewar sanarwar, “Hankalin Kwamishinan ‘Yan sanda, Kwamandan Jihar Oyo, CP Joe Nwachukwu Enwonwu, ya koma kan abubuwa biyu da suka faru a Idere da ke yankin Karamar Hukumar Ibarapa ta Tsakiya, inda wata ’yar kasuwa da ‘yar shekara biyu- wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kashe wasu ‘yan uwan mahaifin, yayin da aka sace wani mutum mai suna Dakta Akinyele a Tapa dake yankin Karamar Hukumar Ibarapa ta Arewa ranar 2 ga Janairun 2021.
Sanarwar ta ci gaba da cewa “Satar Dakta Akindele a asibitinsa, duk da cewa ba a bayar da rahoto a hukumance ga hedikwatar ‘yan sanda na shiyya da ke Ayete kamar yadda DPO ya fada ba, lamari ne mai matukar damuwa. Duk da haka, ya sake jaddada alkawarinsa na sake fasalin gine-ginen tsaro na yankin (don yin) aiki fiye da na shekarar da ta gabata 2020. Ya bayyana cewa, an dukufa don kare rayuka da dukiyoyi a yankin Ibarapa musamman da kuma Jihar Oyo baki daya.
“Kwamishinan ‘yan sandan yana amfani da wannan dama wajen kara tabbatar wa da kowa da kowa a cikin Jihar Oyo cewa an samar da wadatattun matakan tsaro don kwararru don hana duk wata karya doka da oda a jihar. Ya bayyana cewa mutanen kirki na jihar Oyo an umurce su da gudanar da ayyukansu na halal ba tare da tsoro ko fargaba daga wasu mutane, ko kungiyoyi ba, tare da yin tir da karuwar sace-sace da ake samu a jihar, kuma ana bukatar yawaita kwantar da hankali a cikin ayyukanmu na yau da kullum don dakatar da karuwar lamarin.
“Ya karkare da cewa a matsayinta na sabuwar shekara, rundunar tana bukatar hadin kai tare da hanzarta yada sahihan bayanai daga jama’a yayin da ‘yan sanda kuma za su bayar da kyakkyawan aiki. ”