A jiya Alhamis, kungiyar masu fama da bukata ta musamman da aka fi sanin su da nakasassu da suka fito daga yankin Neja Delta, sun sha ruwan barkonon tsohowa yayin da suka mamaye mashigar majalisar dokoki ta kasa da zanga-zangar kin amincewa da watsi ko ‘sakaci’ da aka yi da su daga wajen wakilansu.
Masu zanga-zangar dai sun shaida cewar sun je majalisar dokokin kasar ne domin bayyana bukatunsu na cewa ‘yan majalisun sun kaza kula da su da rayuwarsu, don haka suka nemi tabbas sai ‘yan majalisar sun sauya yadda suke bi da su domin su ma rayuwarsu take inganta.
Hatsaniyar ta fara kunno kai ce lokacin da masu zanga-zangar suka bukaci ganin ‘yan majalisun da ke wakiltarsu amma hakarsu ta gaza cimma ruwa.
Fusatattun masu zanga-zangar sun danna kai zuwa cikin harabar majalisar duk da tirjisyar da suka samu daga bangaren jami’an tsaron da ke gadin mashigar majalisar.
Yayin da su kuma masu zanga-zangar suka tirje suka dage wajen ganin sai sun shiga har zuwa kwaryar inda majalisa ke zamanta domin neman dai sai sun ga ‘yan majalisun da suke wakiltarsu.
Daya daga cikin shingen binciken korona da aka sanya domin gwajin cutar ga masu shiga majalisar a nan ma dai an buga rashin jituwar a tsakanin masu kula da majalisar da masu zanga-zangar.
Ganau sun shaida cewar jami’an tsaron sun dauki tsawon lokaci su na ta rarrashi da kokarin shawo kan masu zanga-zangar da suka nace kan cewar sai sun isa ga inda ‘yan majalisun suke.
An ce, masu zanga-zangar sun mangare wani jami’in tsaron da ya yi kokarin taresu. Lamarin da ya kai ga tursasa ‘yan sandan harba musu hayaki mai sanya kwalla.
Jagoran masu nakasan da ke wannan zanga-zangar, Emotonghen Azikwe, ya shaida cewar ‘yan majalisar sun ki sauraronsu da ba su damar ji daga garesu duk kuwa da wasikun da suka yi ta aike musu da su.
Ya ce: “A ranar Litinin mun zo nan wajen wanda har shugaban majalisar dattawa ya shiga cikin lamarin ya kuma nemi sanatocin da su ganmu a ranar Talata.
“Amma sun gaza sun kasa cika alkawarin ganinmu.
“Wadannan mutanen su na samun kudade a madadinmu amma sun gaza yi mana komai.
“Sun gaza yin dokokin da za su kare mu, kawai su na yin dokoki ne domin kare kawukansu.
“Dole ne su fara biyanmu dan karamin alawus duk wata kuma su ayyana mana rana ta musamman na kasa,” inji shugaban.
Mataimakin shugaban mai tsawatarwa na majalisar dattawan, Aliyu Sabi Abdullahi, wanda ya jagoranci ‘yan majalisar domin ganawa da masu zanga-zangar, ya rokesu da su kwantar da hankalinsu, yana mai ba su tabbacin za a shawo kan matsalolin da suke da su.
Ya bukaci fusatattun masu zanga-zangar da su wakilta mutum biyar da za su zo a matsayin shugabanni domin gabatar da majalisar bukatunsu.
Ya kuma ba su tabbacin cewa za a shigar da bukatunsu cikin kasafin kudin 2021.