Bello Hamza" />

‘Yan Sanda Sun Tarwatsa Zanga-Zangar ‘Yan Adawa A Benin

‘Yan Sanda a Jamhuriyar Benin sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga zangar adawa da cire sunayen ‘yan adawa cikin ‘yan takarar zaben Majalisar dokokin da za’ayi ranar 24 ga watan Afrilu mai zuwa.
Jam’iyyar USL ta hamshakin dan kasuwa Sebastien Ajabon ta kira zanga zangar wanda ya samu halartar dubban mutane wadanda suka tare babbar gadar da ta raba manyan biranen kasar biyu Cotonou da Port Nobo.
Hukumar zabe da ma’aikatar cikin gida sun ce Jam’iyyar USL ta gaza wajen gabatar da sunayen ‘yan takarar ta kamar yadda dokar zabe ta tanada.
A baya-bayan nan ne dai gwamnatin Benin ta dauki matakin cire sunayen ‘yan adawa daga cikin jerin ‘yan takarar da za su kara a zaben kasar da ke tafe nan da watanni biyu masu zuwa.

Exit mobile version