Rahotanni daga Kasar Italiya sun zo da ingacin cewa a ranar Laraba, akalla mutum 16 ne‘ yan sandan kasar suka kame bayan sun fasa wata kungiyar ‘yan mafia ta wasu ‘yan Nijeriya a garin Trento da ke Arewacin kasar, in ji Kamfanin Dillancin Labarai na ANSA na dake Kasar Italiya.
’Yan sandan a cikin rahoton, sun ce sun kai samame har sau 20 a yankunan Trentino, Beneto da Lombardy a yayin aikin, wadanda aka yi wa lakani da karkashin kasa. ’Yan sanda sun ce wurin da gungun ‘yan kungiyar ke sarrafa ayyukansu wani wuri ne da su ke gudanar da kasuwanci a Trento.
Ko ma dai yaya, shi wannan wuri an kafa shi ne a bayan wani shagon sayar da kaya na kabilun Nijeriya a garin Berona na Beneto, inda Nijeriya ke sana’ar sayar da kayan maye, ‘yan sanda sun ce yayin da aka adana magungunan a wani garin na Beneto, Bicenza.
’Yan sanda sun ce wadanda aka kama din ana zargin sun sauya hanya zuwa Trento da Berona a cikin jirgin. Rahoton ya kara da cewa, ana zargin wata mata ‘yar Nijeriya, Agho Isoken Tina, da ake kira Mama T. da sarrafawa da rarraba shi.
Kwamandan Trento Flying Skuad, Tommaso Niglio, wanda ya jagoranci tawagar da ta farfasa gungun, ya ce da yawa daga cikin masu turawa matalauta masu neman mafaka, ya kara da cewa sau da yawa za su hadiye allurai, suna kasada da rayukansu maimakon fuskantar kamu.
An tattaro cewa ‘yan sanda sun kama rabin kilogram na hodar iblis da tabar wiwi a yayin samamen.