Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

’Yan Sandan Kano Sun Bajekolin Barayi Da ’Yan Damfarar Waya

by Muhammad
January 13, 2021
in LABARAI
3 min read
Damfarar Waya
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Abdullahi Muhammad Sheka,

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano karkashin jagorancin CP. Habu Ahmad Sani ta bayyana nasarar damke wasu barayin wayoyin hannu, wadanda suka kware wajen ta’addanci ga al’ummar Unguwannin Sharada, Sauna da rukunin unguwar Sabon Gari dake birnin Kano.

samndaads

Rahotanni na nuni da cewa, Jihar Kano ce ke da yawan adadin barayin wayoyin hannu, wadanda suka kware wajen kwacen wayoyin hannu a ’yan shekarun da suka gabata, wanda irin wannan ta’addaci ke sanadiyyar rasa rayukan al’umma.

Jawabin haka yana kunshe cikin jawabin da Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya yi wa manema labarai ranar Talatar da ta gabata, inda ya ce, sakamakon yawaitar korafe-korafe daga mazauna wadannan unguwannin da abin ya shafa ke yawan yi wajen karuwar yawaitar sace-sacen wayoyin hannu.

Sauran wadanda ake zargin a cewar kakakin rundunar akwai Mustapha Dahiru mai shekara 18, Ibrahim Salisu mai shekara 22, Najib Ibrahim shekara 28, Dahiru Abdullahi dan shekara 20, Ya’u Abdullahi mai shekara 20, Yusif Sadik mai shekara 18 da kuma Ya’u Abdullahi.

“Kamar yadda aka samu rahoto daga bakin mazauna unguwar Sharada, Sauna da Sabon Gari dake Jihar Kano cewar matsalar kwacen waya, fashi da makami ya mamaye wadannan unguwanni. Don haka Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano, CP. Habu A. Sani, ya bada umarni ga dakarun ’yan sandan kafin kiftawa da bissimillah, wanda SP. Bashir Musa Gwadabe ke jagoranta, domin tabbatar da kame wadanda ake zargin da aikata wannan ta’asa.

“Dukkan wadanda ake zargin sun amsa laifukansu cewar suna cikin tawagar ’yan fashi da makami da barayin wayoyin hannu. Dukkaninsu an kama su dauke da muggan bindugu. Wadanda ake zargin sun amsa laifin cewar suna shaye-shaye muggan kwayoyi,” inji Kiyawa.

Mai magana da yawun da rundunar ’yan sandan ya kara da cewa, samamen ya kuma samu nasarar kame manyan dilolin kwaya da kuma nau’ikan kwayoyin a tare da su, wadanda aka kama suna hada da kai da Umar Sharif mai shekara 25, wanda aka kama dauke da kulli 137 na tabar wiwi, Gambo Idris dan shekara 40, wanda shi ma aka kama da dauke kulli 97 na tabar wiwi, Ghali Alhassan mai shekara 25, wanda aka kama da buhu 11, kwayra Edol da kulli bakwai na Diazepam da kuma Barau Umar, wanda shi ma aka kama dauke da kwali shida na Diazepam.”

Cikin wadanda rudunar ’yan sandan ta yi holensu har da dilolin kayan maye, wadanda ake zargi, inda a cewar Abdullahi Haruna duk sun amsa laifukansu na sayar da kayan maye ga ’yan daba. Sannan kuma an damke wadanda suka kware wajen satar kudade daga asusun ajiyar mutane.

Kiyawa ya ce, tawagar ’yan sandan ta samu nasarar damke wasu mutane shida da ake zargi da satar wayar Samsung Galady kuma suka yi amfani da layin wayar da suka sata wajen cire kudi daga asusun ajiyar mamallakin wayar.

“A ranar 03 ga Oktoba, 2020, da misalin karfe biyar na yamma, wani mai suna Abdulsalam Isah na unguwar Gwagwarwa dake birnin Kano, ya kawo korafin cewa, wasu da ba a san ko su wane ba sun sace masa wayarsa kirar Samsung Galady T5, wadda aka kiyasta kudinta ya kai Naira 180,000.00, haka kuma a ranar 05 ga Oktoba, 2020, wadanda ake zargin suka yi amfani da layin wayar, inda suka cire kudi daga asusun ajiyar mamallakin wayar da suka kai 330,000.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya kuma shelanta kame wasu da ake zargi da suka hada da Kabiru Adamu mai shekara 24 daga Jihar Kaduna, Najib Suraj mai shekara 29 daga unguwar sharada, Naziru Aminu mai shekara 23 adai unguwar ta Sharada, Auwalu Usman shekara 22 daga Jihar Kaduna, Mustapha Mohammed shekara 22 daga rimin kebe da kuma Abdullahi Hussein mai shekara 27 daga unguwar Tudun Murtala a Jihar Kano. Dukkansu sun amsa laifin zargin satar wayoyi da ake masu.

Haka kuma kakakin rundunar ‘yan sandan ya bayyana nasarar da jami’an tsaron farin kaya suka samu na damke Umar Isa mai shekara 19 dan asalin karamar Hukumar Kankara dake Jihar Katsina bisa zargin damfarar wasu mutane, Auwalu Abdumalik da Buhari Yusuf kudi har Naira dubu dari uku da talatin. Haka kuma wadanda ake zargin sunyi barazanar yin garkuwa da mutanen matakar suka gaza kara aika masu da wasu karin kudaden. Abdullahi Haruna Kiyawa yace za’a gurfanar da wadanda ake zargin gaban kotu bayan kammala bincike.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Dalilin Da Ke Kawo Zubewar Gashin Mata

Next Post

Shirin Zamanantar Da Cinikin Lemon Fata Ya Kusa Kankama A Kano – Na’alto

RelatedPosts

Hutun Kirsimeti

Gobarar Sakkwato: Gwamnatin Tarayya Ta Jajantawa Tambuwal

by Muhammad
6 hours ago
0

Daga, Sharfaddeen Sidi Umar, Kakkarfar tawagar Gwamnatin Tarayya ta jajantawa...

An Sace Jami’ar Yaɗa Labarun NIS Reshen Jihar Edo

An Sace Jami’ar Yaɗa Labarun NIS Reshen Jihar Edo

by Sulaiman Ibrahim
9 hours ago
0

Masu garkuwa sun yi awon gaba da jami'a mai magana...

Tsaro: Wasu Gwamnonin Nijeriya Na Ganawa Da Shugabannin Fulani Makiyaya

Tsaro: Wasu Gwamnonin Nijeriya Na Ganawa Da Shugabannin Fulani Makiyaya

by Sulaiman Ibrahim
9 hours ago
0

Yau gwamnonin yammacin Nijeriya ke gudanar da wani taro da...

Next Post
Lemon Fata

Shirin Zamanantar Da Cinikin Lemon Fata Ya Kusa Kankama A Kano – Na’alto

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version