Khalid Idris Doya" />

’Yan Sandan Kano Sun Cafke Mace Mai Garkuwa Da Mutane

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta shaida cewar wata mace ta na daga cikin mutum hudu da suka cafke bisa zarginsu da kasance masu garkuwa da mutane a Kano ranar Juma’ar da ta gabata.

Kakakin ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya shaida wa majiyarmu hakan a jiya Litinin, tare da kara wa da cewa, sun samu nasarar kame wadanda suke zargi da garkuwa da mutanen ne a bisa kokarinsu na tsarkake jiyar daga ayyukan ‘yan ta’adda.
Kiyawa ya ce, maza uku da mace daya ne suka kama bisa zargin sace mutane domin neman kudin fansa.
Ya yi tilawar cewa, ‘yan sandan sun mamaye wani gida a kauyen Jaba da ke karamar hukumar Ungogo a jiyar inda suka kame wasu da suke zargi masu garkuwa da mutane da suke zaune a wajen.
Ya ce, wadanda ake zargi da garkuwan ‘yan asalin jihar Zamfara ne.
Kakakin ‘yan sandan ya ce, sun gano macen ta kama hayar gidan ne a kan kudi naira 600,000 a shekara guda a hannun jami’an da ke bada hayan gida.
Kakakin ya kara da sun gano cewa macen ta shiga harkar garkuwa da mutane ne bayan da aka kashe mata mijinta a Zamfara.

Exit mobile version