Connect with us

LABARAI

‘Yan Sara-Suka Sun Latata Motoci Da Babura 78 A Jos

Published

on

A jiya ne Jami’an Tsaro a jihar Filato suka samu nasarar cafke wasu matasa masu tada zaune zaye da daman gaske waxanda aka fi saninsu da suna ‘yan Sara-Da-Suka, waxanda suka lalata motocin jama’a guda 35 haxe da Babura jama’a guda 39 a cikin karamar hukumar Jos ta Arewa, a wani harin da suka kai.
‘Yan daban waxanda suka fita wani ofereshen mai suna ‘Shara’ wanda suke mangare dukkanin abun da suka tarar ko da kuwa mutum ne a lokacin da suka kai wannan farmakin nasu zuwa wata unguwa, inda kuma da misalin karfe 2 na safiyar ranar ne suka suka kai wannan farmakin inda suka tunkari layuka guda uku da suke kan layin Bauchi Rod a cikin jihar ta Filato.
“Sun haura layin Congo-Russia suka nausa zuwa Bulbula, kana suka gangaro zuwa layin Dan-Maraya daga bisani suka gangaro zuwa Bauchi Rod. Motocin jama’a da dama sama da 35 da mashina sama da 39 ne suka lalata wa jama’a,” In ji Kwamadan kula da jin daxin jama’a na kungiyar ‘yan Banga (BGN) Ahmad Mudi said.
Mudi, ya shaida cewar ‘yan sara-sukan sun ganu da fushin jami’an tsaro ciki kuwa har da ‘yan sanda, inda suka samu nasarar kame matasan da dama.
Jami’in watsa labarai na ‘Operation Safe Haben’, Major Adam Umar, ya ce, ya shaida cewar ba zai iya bayyana adadin waxanda suka cafke a halin yanzu ba, amma ya shaida cewar sun kame su da wasu makamai haxin gida.
Major Umar ya shaida cewar suna ci gaba da gudanar da bincike kan waxanda suka kame haxe da zarginsu kan wannan lamarin, don haka ne za su gurfanar da su a gaban kuliya bayan kammala gudanar da bincikensu.
Advertisement

labarai