Bello Hamza" />

‘Yan Shi’a Sun Nisanta Kansu Daga Goyon Bayan Buhari

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci a Nijeriya, wadda aka fi sani da ‘yan shi’a sun nisanta kansu daga wasu rahotannin dake yawe a kafafafen yada labarai wanda ke cewa, wai kungiyar ta mika goyon bayan ta ga takarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben da ake shirin gudanarwa ranar 16 ga watan Fabrairu 2019.
Kungiyar ta bayyana haka ne a takardar manema labarai da Malam Shu’abu Isa Ahmad na dandalin dalibai (Academic Forum) ya sanya wa hanun, inda ya kuma kara da cewa, kungiyar ta barranta da bayanin dake yawo ina aka ce wai sun mika goyon bayan su ga takarar Shugaba Buhari da Gwamna Masari na jihar Katsina da kuma Gwamna Ganduje na jihar Kano, ya na mai cewa, wannna labarin kanzon kurege ne, an kuma yada labarin ne don a bata sunan kungiyar a daidai wannnan lokacin ake harkokin zabe a kasar nan.
Shu’iabu ya kuma bayyana cewa, a bayyana yake cewa, kungiyar a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky ya yi shekara fiye da arba’in yana gwagwarmayar tabbatar da musulunci ba tare da daukar makami ko tayar da hankalin kowa ba, kuma ba a taba samun labarin kai tsaye mun shiga harkar goya wa wani dan siyasa baya ba a kan mukamin da yake nema ba,” inji shi.
Daga nan ya kuma tunatar da cewa, a ranar 12 ga watan Disamba na shekarar 2015 bayan wani sabani, sojojin Nijeriya suka kai hari gidan Shaik Ibraheem Zakzaky inda suka hallaka magoya bayansa fiye da mutum da 1000 tare da kuma lalata wuraren ibadunmu, haka kuma bai sa mun dauki matakin tayar da hankali ba, wanda kuma har yanzu yana hannun jami’an tsaro tare da matarsa duk da wata babbar kotun tarayya karkashin shugabancin Mai Shari’a Gabriel Kolawale ta bayar da umurnin sakinsa ba tare da wani sharidi ba.
Abin lura a nan shi ne, in har miliyoyin masu goyon bayan Shaih Zakzaky za su yi amfani da kuri’asu mai zai sa su jefa wa wanda a karkashinsa aka kashe su?’, in ji shi.
Ya kuma kara da cewa, kungiyar tana mika godiya ga dukkan ‘yan Nijeriya wadanda suka tsayu tare da goyon baya ga Shaikh Zakzaky da jama’arsa, a kan haka “A kan haka ne muke kira ga sauran ‘yan siyasa da su yi koyi da dan takarar shugabancin kasar nan na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar a bisa yadda ya yi tir da zaluncin ca ake yi wa Shaikh Zakzaky da jama’arsa.
Muna kuma amfani da wannna dama na kira da a saki Shaikh Zakzaky da matarsa Zeenah Ibraheem da Deji Adeyanju da kuma sauran ‘yan Nijeriya da suke garkame a fadin tarayyar kasar nan,” inji shi.
Daga karshe Shu’aibu Ahmad ya bukaci ‘yan Nijeriya su rungumi tafarkin zaman lafiya, musamman a daidai wannan lokaci da ake shirin gudanar da zabe kasa na 2019.

Exit mobile version