Connect with us

RIGAR 'YANCI

’Yan Shi’a Sun Yi Zanga -zangar Lumanar Neman Sako El-Zakzaky A Lokoja

Published

on

Daruruwan mabiya kungiyar mazahabar Shi’a ta Islamic Mobement of Nigeria ( IMN) a ranan juma’ar data gabata a birnin Lokoja, sun gudanar da wata zanga zangar lumanan neman sako Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

Bayan an sauko juma’a ne dai mabiya kungiyar ta IMN suka taru a babban masallacin juma’a da ke garin na Lokoja dukkansu dauke da kwalayen rubuce rubucen kira ga gwamnati data gaggauta sako shugaban nasu ganin cewa tuni kotu ta bada umurnin sako shi.
Da ya ke zantawa da wakilin jaridar LEADERSHIP A YAU kadan bayan sun kammala zanga zangar, mai magana da yawun kungiyar, Malam Saidu Ali Ja, yace idan lallai gwamnati na son tayi adalci kuma tana ikirarin mai bin doka ne, kenan ya zama wajibi gwamnatin ta gaggauta sako Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da uwargidansa,malama Zinatu wadanda a yanzu su ke tsare a hannun gwamnati.
Malam Ali Ja wanda ya jagoranci sauran mabiya mazahabar shi’ar wajen gudanar da zanga zangar inda suka rika bin unguwannin garin Lokoja, yace zasu ci gaba da gudanar da zanga zangar har sai an sako shugaban nasu da kuma mai dakinsa.
Mai magana da yawun kungiyar ta IMN kazalika ya kalubalanci gwamnatin tarayya data jihar Kaduna dasu bi umurnin kotun idan har sun ikirarin a mulkin dimukradiyya ake yi a Nijeriya wanda ya bada yancin yin addini.
Malam Ali Ja ya kuma yi Allah wadai da kisan gillar da gwamnati take yawan yiwa dimbin magoya bayan kungiyar ta IMN a sassa damban dabam na kasar nan, inda kuma babu gudu babu ja da baya, har sai an sako shugaban nasu, wato Sheikh El-Zakzaky.
Daga bisani ya godewa daruruwan mabiyar kungiyar dasu ka fito kwansu da kwarkwatansu, domin gudanar da zanga zangar.
Advertisement

labarai