Ammar Muhammad" />

‘Yan Siyasa Ke Dagula Tsaron Kasarnan, Inji Burutai

Shugaban Hafsan Sojojin Nijeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya yi zargin cewa ‘yan siyasa ne suke dagula lamarin tsaron kasarnan. Ya yi wannan zargin ne a yayin da yake jawabi ga membobin kwamitin kula da harkokin sojoji na majalisar wakilai ta Nijeriya wadanda suka je Maiduguri fadar jihar Borno domin samun bayanai a kan yadda ake samun tabarbarewar tsaro a Nijeriya.

Babban hafsan Sojin Nijeriyar Laftanar ya ce; ‘yan siyasa da suka fadi zabe na da hannu wajen karuwar hare-haren ‘yan bindiga da sace mutane a yi garkuwa da su don neman kudin fansa wanda ake fama da shi a shiyyoyin Arewa maso Yammaci da Arewa ta Tsakiya.

“Kalubalen tsaro da muke fuskanta yanzu haka, ina da yakini cewa ba za a rasa alakanta shi da zaben da aka kammala ba da dadewa ba, wasu ‘yan siyasa da suka fadi zabe na daukar nauyin ayyukan na bata gari muna da shaidu masu karfi, sai dai muna taka-tsantsan don kauce wa kuskure.”

Exit mobile version