Daga El-Mansur Abubakar, Gombe
Ibrahim Yusuf, shi ne jagoran kungiyoyi masu zaman kansu wadanda ba na gwamnati ba NGOs a Gwambe shi ne ya bayyana cewa akwai Mata ‘yan siyasa da yawa a jihar Gwambe amma sun gagara taka kowacce irin rawa dan ganin an shawo kan cin zarafin ‘Ya’ya Mata ta hanyar yi musu fyade da ya zama ruwan dare a jihar.
Ibrahim Yusuf, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Gwambe inda yace, a baya kungiyoyi irin nasu na NGOs suna tsayawa wajen yin fafutukar ganin sun sa baki don yin kira a bai wa Matan kashi 30 cikin dari na mukaman gwamnati da suka jima suna neman a basu amma su kuma basu taba fitowa don sauraron koken mata ‘yan uwansu ba.Yace, ana yawan samun matsalar yiwa yara kanana fyade a kauyuka har ma da cikin gari da sukan shiga suga an kamo an masu yin fyaden an hukuntasu dan haka ya zama izna ga masu sha’awar aikata hakan amma su matan da ake dasu suke rike da mukaman siyasa basu taba hada kansu don taimakawa Yaran ba duk da kasancewarsu Iyaye.Ya kuma ce mafi yawan Yaran da suke fuskantar irin wannan matsala ta fyade ‘ya’yan Talakawa ne wadanda iyayensu ba za su iya yin komai akai ba balle su kai rahoto ga wata hukuma.
Ibrahim Yusuf, yace, yanzu a jihar Gwambe akwai mata Kwamishinoni guda hudu, akwai ’Yar Majalisar Tarayya banda Mata masu taimakawa gwamna na musammam, akwai Manyan Sakatarori hudu Mata ne ga Daraktoci da ake dasu amma duk da haka basu taba fitowa da murya daya don neman ganin sun tsayawa irin Yaran da aka yiwa fyade don nemo musu yancin ba.“A dunkule basu taba fitowa da sunan muryar Matan Gwambe don kwatowa Yaran ’Yancin ba haka a dai dai kunsu ba wata mace da ta taba fitowa don yin magana ba duba ga cewa su mata ne iyaye”A cewarsa da za su yi haka koda sau daya ne da sun ajiye wani tarihin da ba a taba yin irinsa ba a Gwambe amma ba suyi ba, idan sun ce sun taba yin kalubalensu su fito su fada duniya tayi shaida.
Ibrahim Yusuf, ya ci gaba da cewa, sune a zamansu na kungiyoyin da bana gwamnati ba idan suka samu irin wannan rahoto suke tashi subi diddigin labarin sannan su kai wa jami’an ’yan sanda rahoto su taya su daga bisani akai mai laifin kotu.Yace, a lokacin da suke gudanar da aikace-aikacensu suna hada kai da Kungiyar Mata Lauyoyi da takwararta ta mata ’yan Jarida NAWOJ da kuma jami’an farin kaya na Cibildepence don tabbatar da an kwato wa yaran ’yancinsu da aka take musu hakki.
Daga nan sai ya yi amfani da wannan damar ya kirayi iyayen Yara da cewa duk Uban da aka yiwa ’yarsa fyade kar ya boye ya fito ya bayyana domin boyewar ba alheri bane yana jawo matsala a gaba lokacin da aka gano cewa an yiwa yar fyade bayan baa samu hujjar da zaa kama wanda ya yi din ba.