Daga Muhammad Awwal Umar
Honarabul Murtala Abdullahi Falasko shi ne mataimakin jami’an hulda da jama’a na jam’iyyar APC a karamar hukumar Gudu ta jihar Sakkwato, a takaitaccen hirarsa da LEADERSHIP A Yau, ya ce matakin da ‘yan siyasa ke dauka a karamar hukumarsa kokari ne na mayar da hannun agogo baya a siyasan ce.
Honarabul Falasko ya bayyana cewa: “Maganar gaskiya ba abu ba ne mai kyau, domin da ‘yan sisayar sun san abin da suke yi da ba akan dan majalisa za a yi zanga-zangar ba. Domin tun bayan kammala zabukan kananan hukumomi ashirin da biyu cikin kananan hukumomi ashirin da uku da muke da su, sannan mu jama’ar karamar hukumar Gudu da gwamnatin jiha ta gudanar da wannan zabukan amma ba a yi na karamar hukumarmu ba har yanzu kuma ba a ce mana komai ba mu kai biyayya ga shi kantoman riko da maigirma gwamna ya nada mana, da cibgaban suke so da gaske ya kamata ne ‘yan siyasar su tunatar da maigirma gwamna cewar har yanzu fa ba a yi zabe a karamar hukumarmu ba.
“Honarabul Sani dan majalisar dokokin jiha mai wakiltar Gudu ko a majalisar tarayya yake abin da yake yi yanzu ya can-canci a yaba ma sa. Domin shi mutum ne marar tsoro kuma ya tsaya akan hakkin talaka, amma idan akwai wasu makiya ta bayan fage da ke son ganin bayan karamar hukumar Gudu ta ba zan yi musu ba, abin mamaki da takaici shi ne kujera daya da muke alfahari da shi a wannan majalisar ana mana zagon kasa a kansa.” In ji shi.
“Shawarar da ni ke baiwa jama’ar Gudu, kar su yarda da ‘yan a fasa kowa ya rasa, kar su yarda da masu kokarin gurgunta karamar hukumar mu. Sannan ina jawo hankalin gwamnatin jiha kan muhimmancin zaben karamar hukumar Gudu, dan mu ma muna da hakkin kamar kowani dan jihar Sakkwato, maigirma gwamna ya tausaya mana, ya ba mu damar mu ta siyasa mu ma mu taka na mu rawar ganin ga jama’ar mu.” In ji Falasko