Khalid Idris Doya" />

‘Yan Siyasa Suna Barazana Wa Rayuwata, Inji Maryam Bagel

‘Yar majalisar dokokin jihar Bauchi, mai wakiltar mazabar Dass, Hajiya Maryam Garba Bagel ta bayyana cewar wasu mutanen da ba ta kai ga ganosu ba suna yi wa rayuwarta barazana, don haka ne take shelanta wa jama’a, inda ta nuna cewar hakan na daga cikin yunkurin magaftanta ‘yan siyasa da suke jihar.

Maryam Bagel wacce take shaida hakan wa ‘yan jarida a gidan a ranar Talata, ta shaida yadda lamarin ya fara riskarta, “A ranar Litinin din da ta gabata da yammaci bayan na dawo daga gidan ‘yar uwata a lokacin da muke shirye-shiryen bukukun sallah, wani ya kirani a waya ya boye lambarsa ya shaida min cewar akwai wasikar da ya ajiye min a gidana.

“Lokacin da na kira mai bani kariya kan wannan ambulof din da aka aike min da shi gida, abun da na gani a ciki ya firgitani, domin wasikar ta cikin ambulub tana dauke ne da hotuna, wasu hotuna da aka tattaro daga turakata ta facebook, da kuma wasu hotuna marasa kan gado da aka hada a ciki, hadi da tattaunawar hira da ba baina mai amsawa ba,” A cewar ta

Bagel wacce a baya-bayan nan ta tsaya neman kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu a karkashin jam’iyyar SDP, ta kara da cewa, wuraren karfe sha daya na dare a wannan rana ta Litinin, wanda ya kirata da boyeyyen lambar ya sake kiranta, inda ke mata gargadin ta yi kokarin daina cakalar gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar ko kuma ya yi hanzarin daukan mataki a kanta.

Ta kara da cewa; mutumin da ke ci gaba da bibiyarta ya ci gaba da zayyana mata ka’idarsa ko kuma ya dau mataki a kanta, inda take shaida cewar ya kuma aike mata da sako ta kafar WhatsApp inda ke neman ta sauya halinta ta yi wa gwamnan Bauchi biyayya ko kuma rayuwarta ya kasance a cikin garari.

Maryam ta kara da cewa, makamancin irin wannan sakon da ke mata barazanar ya shiga wayar mijinta, inda ake jan kunnensa da ya taka wa matar tasa burki kan ababen da take yi na adawa, hadi da ta dawo cikin biyayya ga wanda mai tura mata sakon ke son ta yi wa biyayya.

Shi ko kin sanar da jami’an ‘yan sanda da sauran bangarorin tsaro kan halin da kike ciki? sai ta amsa da cewa, “Allah ne mai kareni, ni sam ban firgita ba kuma ina da yakinin Allah zai kareni a kowani bigire,” A cewar ‘yar majalisar.

 

 

Exit mobile version