CRI Hausa" />

’Yan Siyasar Amurka Ne Ke Boye Tsananin Yaduwar Annobar COVID-19 A Kasarsu

A yayin da wasu ’yan siyasar Amurka ke kara dora wa wasu laifin tsanantar yaduwar annobar COVID-19 a cikin kasar, Shi kuwa Mike Pompeo, sakataren harkokin wajen kasar Amurka ya sake shafa wa kasar Sin kashin kaji a ranar 8 ga wata, inda a cewarsa, kasar Sin ta boya adadin mutanen da annobar ta shafa. Ko da yake bayanan da hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato WHO da mujallar Kimiyya suka gabatar, sun tabbatar da gaskiyar adadin da kasar Sin ta bayar, amma ’yan siyasar Amurka sun kau da kai, suna kokarin dorawa kasar Sin laifi, sun yi fatali da shaidun kimiyya. A ganinsu, siyasa ya fi ceton rayukan mutane muhimmanci.

Hakika, wasu ’yan siyasar Amurkawa ne suka boye bayanan yaduwar annobar. Ba su yi tunanin asarar dukiyoyi da rayukan mutane da abubuwan da suka aikata suka haddasa ba, maimakon haka, sun dora wa kasar Sin laifi. Wannan rashin da’a ne sanin ya kamata.
Hukumar WHO ta musunta zargin da aka yi wa kasar Sin dangane da bayanan da kasar ta bayar. Michael J. Ryan, jami’in kula da ayyukan gaggawa na hukumar ya yi nuni da cewa, bayanan da ya duba game da nazarin kwayoyin cutar ta COVID-19 sun hada da guda daga kasar Jamus, wani daga kasar Singapore da wani daga Amurka, kuma wasu 4 daga kasar Sin.
Dalilan da suka sa kasar Sin ta dakile yaduwar annobar cikin watanni 2 ko fiye da haka, su ne domin jam’iyyar da ke mulkin kasar ta tsai da kuduri ta hanyar kimiyya, ta kuma tura ma’aikatan lafiya zuwa birnin Wuhan da ma lardin Hubei baki daya daga sassa daban daban na kasar. Har ila yau an hana shigi da fici a wuraren da aka samu barkewar annobar cikin lokaci. Kana, jama’ar Sin biliyan 1.4 sun bi umarnin gwamnati sun yi zama a gida don hana yaduwar cutar, inda suka killace kansu na kusan watanni 3 a gida.
Wasu na shakkar cewa, don me yawan mutanen da suka mutu da jimillar masu kamuwa da annobar a kasar Sin bai kai na kasashen waje ba? A ranar 7 ga wata, Gauden Galea, wakilin WHO a kasar Sin ya yi karin bayani cewa, dalilin da ya sa haka shi ne kasar Sin ta fadada yin gwajin kamuwa da kwayoyin cutar a tsakanin jama’arta. Wannan ya nuna cewa, kasar Sin ba ta boye kome ba kan bayananta.
Yanzu haka yawan wadanda suka mutu sakamakon kamuwa da annobar ta COVID-19 a Amurka, ya wuce dubu 16. Shafa wa kasar Sin kashin kaji da dora mata laifi, tamkar bata lokaci ne, kuma ci gaba da yin karya zai haifar da karin asarar rayuka. A don haka, wajibi ne wasu ’yan siyasar Amurka su mayar da hankalinsu kan ceton rayukan mutane maimakon fadan abin da bai dace ba. (Mai Fassarawa: Tasallah Yuan)

Exit mobile version