Khalid Idris Doya">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

’Yan Ta’adda Na Kai Hari Makarantu Ne Don Kunyata Gwamnati Kawai – Lai

by Khalid Idris Doya
December 23, 2020
in LABARAI
3 min read
’Yan Ta’adda Na Kai Hari Makarantu Ne Don Kunyata Gwamnati Kawai – Lai
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Ministan labarai da al’adu na Nijeriya, Alhaji Lai Muhammad, ya shaida cewar, ’yan ta’adda na kai hari makarantu, don yin garkuwa da kananan yara ne, domin jawo wa gwamnatin kasar abun kunya da zubar da kimar kasar ne kawai, amma ba domin sun san za su yi wata nasara mai dorewa ba.

Lai ya na yin martani ne kan sacewa tare da kubutar da daliban makarantar Kankara 344 da kuma ’yan makarantar islamiyya 80 duka a Jihar Katsina tare da dalibai mata ’yan makarantar Dapchi a Jihar Yobe su 110 a shekarar 2018.  
Ministan, wanda ya yi wata ganawa ta musamman da kamfanin Dillacin Labarai ta Nijeriya (NAN) ya shaida cewar, hare-haren da a ke kai wa makarantu da gangan ake yin su, domin jawo hankalin kasashen duniya.
Ya ce, duk da halin da ake ciki, gwamnatinsu ta fi gwamnatin baya wajen mayar da hankali a bangaren kula da tsaro da kare rayukan ‘yan kasa, inda ya ce, tun lokacin da aka sace ’yan makarantar Kankara gwamnatinsu ta gagara zaune ta kasa tsaye har sai da aka ’yanto daliban.
Lai ya ce, “wadannan dukkanin ’yan ta’addan su na so ne kawai su zubar wa Gwamnatin Nijeriya da kima da mutunci a idon duniya tare da jawo hankalin gaba dayan kasashen duniya.
“Manufar ita ce, su nuna wa duniya cewa dukkanin kasar da ta gagara gami da kasa karewa da kiyaye raunanan cikinta, to wannan kasar gwamnatinta ta gaza kuma bai wa ’yan kasa kariya,” ya shaida.
Ministan kodayake ya jinjina tare da yaba wa hukumomin tsaron kasar bisa hadin kai wajen yin aiki tare, aiki da kwarewa, kaifin basira da hikimomi da suka sanyawa wajen tabbatar da ceto yaran da aka yi garkuwa da su.
Ya ce, a dukkanin duniyar nan babu wata kasa da ta tsarkaku daga ayyukan ‘yan ta’adda kwata-kwata, sai dai a ce na wasu yankin ya fi na wasu kamari. Ya yi nuni da cewa a kasar Amurka ma ana samun mace-mace da kashe-kashe, da kuma kasashe da dama da ‘yan ta’adda ke haifar da matsaloli.
“kasar Amurka duk da fasahohinta da kwararrunta amma ta gaza kare rayukan yara kusan 200 da aka yi ta kashewa da jikkatawa a makaratu daga 2010 zuwa yau. kungiyar MH13, kungiyar asiri ce da ke da cibiya a Lon Angeles, ta addabi Amurka tsawon lokaci. Faransa ta rasa sama da mutane 289 bisa ayyukan ‘yan ta’adda daga 2010 zuwa yau. Ko a baya-bayan nan, a watan Maris 2019, mutum 49 ne aka harbe tare da kashewa a New Zealand.”
Ministan ya kuma shaida cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zo kan gwamnati ne tare da gadar matsalar ‘yan bindiga da na Boko Haram.
Ya ce, matakan da gwamnati mai ci take bi wajen yaki da matsalar tsaro, ya wuce irin wanda gwamnatin baya ta bi sosai nesa ba ma da kusa ba.
“A 2014 da aka yi garkuwa da daliban Chibok a jihar Borno, sai da aka dauki tsawon mako uku kafin gwamnati ta dauki wani matakin da ya dace a kan batun.”
“Mu kuma a bangarenmu ba mu tsaya wani jira ba, mun tursasa, mun matsa har sai da aka ceto yaran nan,” a cewarshi.
Dangane da darussan da su ka koya daga wannan sace yaran, ministan ya shaida cewar an shawarci gwamnatocin jihohi da su kasance a ankare a kowani lokaci kana su kara zage damtse.
Daga nan ya bada tabbacin gwamnati mai ci na cewa za ta cigaba tare da kara kyautata alakarta da jami’an tsaro domin yin aiki tare wajen tabbatar da kare rayuka da dukiyar ‘yan kasa a kowani lokaci.

samndaads
SendShareTweetShare
Previous Post

Nda-Isaiah (1962-2020): Yau Za A Fara Bankwana Da Ciyaman

Next Post

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Garin Minjibir A Jihar Kano

RelatedPosts

Kananan Hukumomin Jihar Kano

Yau Za A Yi Karon Batta A Zaben Kananan Hukumomin Jihar Kano

by Khalid Idris Doya
1 hour ago
0

 Jam’iyyu 11 ne za su fafata PDP Kwankwasiyya ta ce,...

Sojoji

Tsofaffin Sojoji Sun Nemi Karin Kudin Fansho

by Khalid Idris Doya
1 hour ago
0

Kungiyar tsofaffin sojoji ta kasa reshen jihar Anambra ta bukaci...

Ali Baba

Zaben Kananan Hukumomi: PDP Kwankwasiyya Ta Maka KASEIC A Kotu

by Khalid Idris Doya
2 hours ago
0

Bangaren Kwankwasiyya na jam'iyyar PDP a jihar Kano, ta jadadda...

Next Post
Ebonyi

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Garin Minjibir A Jihar Kano

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version