Connect with us

KASASHEN WAJE

‘Yan Ta’adda Sun Kai Hari A Iran

Published

on

Da safiyar yau ‘yan ta’addan da ba a gane su waye ba suka kai harin ta’addanci yayin da taron tunawa da ‘yan mazan jiya yake gudana a garin Ahwaz kudu masu yamma na kasar Iran.

Ance adadin mutanen da suka rasa ransu ya kai 25, cikinsu akwai yara kanana, mata da kuma ‘yan jarida, ‘yan ta’addan sun bude wuta kan mai-uwa-da-wabi ne a daidai lokacin da taron yake tsakiyar gudana.

Ance ‘yan ta’addan sun yi shigar basaja irinta soji, sannan sun boye bindigun da suka yi amfani dasu wajen kai harin a gefen wani waje kusa da filin da za a gudanar da taron.

Sojin masu kare juyin juya halin Musulunci na kasar sun sama nasarar hallaka biyu daga cikin ‘yan ta’addan, yayin da suka bazama don neman sauran.

Advertisement

labarai