Connect with us

MANYAN LABARAI

’Yan Ta’adda Sun Kashe Basarake A Kebbi

Published

on

A jiya ne ‘yan ta’addar da ba a san ko su waye ba su ka yi wa basaraken gargajiya a Jihar Kebbi kisan gilla a kan hanyar Dabai zuwa Mahuta da ke yankin karamar hukumar mulki ta Fakai a cikin Masarautar Zuru.

Bisa ga bayanan da ke fitowa daga bakin iyalin marigarin, Alhaji Umar Muhammad, wanda yaya ne a ga mamacin, ya ce, “Sarkin Kudun Bajida, Alhaji Musa Muhammad Bahago kanena ne, ya na kan hanyarsa ta koma wa garinsa na Bajida daga garin Zuru sai wasu ‘yan ta’addan da ba a gane ko su waye ba ne su ka yi ma sa kwanton bauna, inda su ka tare shi yayin da ya ke tuka motarsa shi kadai su ka kama shi su ka kuma fito da shi kasa a dajin bakin hanyar Dabai zuwa Mahuta su ka yi ta saran sa har sai da ya mutu, sannan su ka ranta a na kare ba tare da kama su ba.”

Ya cigaba da cewa, Sarkin Kudun Bajida shi ne kuma Uban Kasar Bajida a Karamar Hukumar Mulki ta Fakai a Masarautar Zuru da ke a Jihar Kebbi. Haka kuma basaraken dan Shekaru 56 da haifuwa a duniya ne kafin mutuwarsa.

“Ya mutu ya bar mata hudu da kuma yara masu yawa,” in ji yayan marigarin basaraken.

Bugu da kari wakilin LEADERSHIP A YAU ya samu jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Kebbi, DSP Nafi’u Abubakar, wanda ya ce, “lallai wannan lamarin ya faru, kuma wannan abin bakin ciki ne da kuma ban takaici kan faruwar irin wannan lamarin.

Ya cigaba da bayyana yadda lamarin ya faru, inda shi ma ya ce, “basaraken ya fito ne daga garin Zuru zuwa Bajida, inda ya ke sarauta a matsayinsa na Uban kasar Bajida, a cikin motarsa, wanda shi ne ya ke tuka kansa. Daga nan ne a kan hanyar Dabai zuwa Mahuta ‘yan ta’addan da ba a san ko su waye ba, su ka yi ma sa kwanton bauna su ka fito da shi daga cikin motarsa, sai su ka kashe shi.”

Bugu da kari DSP Nafi’u ya ce, “jami’an rundunar ‘yan sandan Kebbi sun fantsama fagen farautar neman ‘yan ta’addan da su ka aikata wannan aikin ta’addanci na kashe Sarkin Kudun Bajida, Alhaji Musa Muhammad Bahago, wanda in sha Allah rundunar ‘yan sandan za ta yi iya kokarinta na tabbatar da ta cafke wadannan ‘yan ta’addan.”
Advertisement

labarai