Wasu yan ta’adda wadanda ake zargin suna da alaka da kungiyar ISWAP reshen Boko Haram, sun yi amfani da bam wajen tarwatsa gadar Mandafuma, wadda ke kan hanyar Biu zuwa Damboa, a jihar Borno, da misalin karfe 2:20 na wayewar ranar Talata.
Kamar yadda majiyar mai sharhi kan al’ammuran tsaro, Zagazola Makama ya bayyana a shafinsa, ya ce fashewar ta lalata gadar gaba ɗaya, sa’ilin da ta yanke hanyar wadda ta raba tsakanin kauyen Mandafuma da garin Biu.
Ya kara da cewa, wannan harin ta’addanci an aiwatar da shi ne domin kawo cikas a sha’anin zirga-zirgar jama’a, da motoci, tare da hana sojoji tare da sauran jami’an tsaro shiga yankin.