‘Yan Wasan Arsenal Sun Bawa Duniya Kunya

Arsenal's Swiss midfielder Granit Xhaka (2L) restrains Tottenham Hotspur's Belgian defender Jan Vertonghen (L) and Arsenal's English midfielder Theo Walcott (3L) during the English Premier League football match between Arsenal and Tottenham Hotspur at the Emirates Stadium in London on November 6, 2016. / AFP / BEN STANSALL / RESTRICTED TO EDITORIAL USE. No use with unauthorized audio, video, data, fixture lists, club/league logos or 'live' services. Online in-match use limited to 75 images, no video emulation. No use in betting, games or single club/league/player publications. / (Photo credit should read BEN STANSALL/AFP/Getty Images)

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Tsohon dan wasn kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Gary Neville, dan kasar ingila, ya bayyana cewa yan wasan kungiyar Arsenal sun bawa duniya kunya kuma sun aikata abin kunya a wasan da sukasha kashi a hannun Manchester City daci 3-0 a wasan karshe nacin kofin Karabawo da suka fafata.

Nebille yace, sun tafka abin kunya sosai kuma sun wulakanta dubban magoya bayansu da sukaje har birnin Landan domin kallon wasan.

Yaci gaba da cewa yadda yan wasan kungiyar suka buga wasan abin kunya ne domin sun buga wasa kamar ana musu dole sannan kuma kamar basason buga wasan kuma basu dage ba domin sun nunawa duniya cewa sun cancanta da zuwa wasan karshen.

Yaci gaba da cewa yan wasan kungiyar kawai sun dinga yawo a filin Wembley ne suna gudu batare da sun san abinda suke bugawa ba saboda babu kishi da zuciya a zuciyaoyinsu.

Ya kara da cewa yanzu a matsayinsa n amai sharhi akan wasan kwallon kafa baya sha’awar kallon wasan Arsenal domin basa burge kowa kuma basa buga wasan daya kamata ace suna burge mutane.

A karshe yace kungiyoyin Tottenham da Liberpool sunfi Arsenal sanin abinda yakamata a fili sannan kuma ba’a maganar kungiyoyin Manchester City da Manchester United da Chelsea domin yanzu sun wuce tunanin Arsenal.

A karshe ya bayyana cewa dole akwai garambawul sosai a kungiyar idan har ana bukatar kungiyar taci gaba da kare kambunta na zama babbar kungiya sannan kuma taci gaba da lashe kofuna.

Exit mobile version