Abba Ibrahim Wada" />

’Yan Wasan Chelsea Su Na Son Lampard Ya Zama Kociyan Kungiyar

Da yawa daga cikin ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da kuma ragowar masu koyar  da kungiyar a yanzu suna fatan kungiyar ta dauki tsohon dan wasanta, Frank Lampard domin ya maye gurbin Mauricio Sarri, wanda zai koma Jubentus.

Sarri dai ya taimakawa Chelsea ta kammala kakar wasan data gabata a mataki na uku kuma ya lashe gasar kofin Europa da kungiyar sai dai duk da haka ya bayyanawa kungiyar cewa zai koma zakarun kasar Italiya wato Jubentus domin ya cigaba da koyarwa  a can.

Tun farkon fara rade radin cewa Sarri zai bar Chelsea aka fara tunanin Lampard shine wanda kungiyar yakamata ta nema domin zama kociyan kungiyar bayan daya kusa kai kungiyar Derby County gasar firimiya ta bana kafin suyi rashin nasara a hannun Aston Billa.

Kamar yadda wani dan jarida, Dean Jones ya tabbatar da yawa daga cikin ‘yan wasa da masu taimakawa mai koyarwa suna son tsohon dan wasan ya koma domin koyar da ‘yan wasan Chelsea sai dai shugabannin kungiyar basu gama gamsuwa da kwarewar Lampard din ba.

Sai dai wasu daga cikin tsofaffin ‘yan waasan kungiyar irinsu John Terry sun bayyana cewa abune mai kyau kungiyar ta bawa Lampard aikin kungiyar sai dai kuma bai taba koyar da wata kungiya a gasar firimiya ba wanda hakan zai iya zama matsala a wajensu.

Lampard dai har yanzu yana da ragowar kwantiragin shekara biyu a kungiyar Derby County kuma a kwanakin baya ya bayyana cewa yana jin dadin aiki da kungiyar saboda haka idan bai samu wata kungiya a gasar firimiya ba zai cigaba da aiki da kungiyarsa.

Exit mobile version