‘Yan Wasan Nijeriya 8 Da Za Su Haska A Gasar Cin Kofin Duniya

Daga: Abba Ibrahim Wada Gwale, 08060119869

Bayan Nijeriya ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a kasar Rasha a shekara mai zuwa, yanzu haka kuma kallo ya koma kan ‘yan wasan da mai horar da su Gernot Rohr, don sanin wadanda zai gayyata, sannan bayan sun je ya za a yi su taimakawa tawagar Super Eagles.

Duk da cewa zuwa yanzu mai koyar da ‘yan wasan bai tantance wadanda zai tafi da su ba, amma akwai ‘yan wasan da babu ko tantama za su tsinci kansu cikin ‘yan wasan da za a gayyata domin wakiltar kasar.

Kawo yanzu dai za mu iya cewa akwai kwararrun ‘yan wasa wadanda ke bugawa Nijeriya wasa kuma suna bugawa manyan kungiyoyi a Nahiyar Turai.

Kamar dai yadda aka sani, wannan dan wasa ne ya maye gurbin N’Golo Kante, wanda ya koma Chelsea daga Leceister City. Kuma kusan wani lokacin ba za ka iya banbance tsakanin Kante da Ndidi ba saboda irin yanayin yadda yake buga wasansa.

Ndidi dai dan wasan tsakiya ne wanda wannan kasa ke bukatar irin sa duk da cewa akwai cewa akwai kwararrun ‘yan wasa da take da su, amma indai ana maganar buga wasa a tsakiya, tabbas Nijeriya ba ta da matsala a kansa.

Ba kasafai aka fiya ganinsa a fili ba, amma idan ana batun bada gudunmawa ko shakka babu wannan dan wasa ba kashin yarwa ba ne. Haka nan idan har mai horar da ‘yan wasan yana da niyyar taka muhimmiyar rawa a gasar cin kofin da aka sanya gaba, ya zama wajibi ya yi amfani da Ndidi.

Idan aka hada shi da Obi a tsakiyar fili, lallai za a sha mamaki ganin yadda suka buga wasan Nijeriya da Argentina, suka  kuma yi matukar kokari.

Kusan sama da shekara goma dan wasan yana wakiltar kasar nan a wasanni daban-daban da kuma gasar kwallaye daban-daban da kasar ta buga a duniya, ciki har da gasar kofin Nahiyar Afrika da kasar nan ta lashe a shekara ta 2013, lokacin da marigayi Stephen Keshi na koyar da ‘yan wasan na super eagles.

Obi, tsohon dan wasan Chelsea ne wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa musu ta hanyar lashe manyan kofuna a tarihin kungiyar.

Ko shakka babu, wannan hazaka da kwarewa da kuma gogewa ta dan wasan za ta taimaka wajen bugawa kugiyar ‘yan wasan (Super Eagle) wasan a zo a cin gasar kofi ta duniya da za a gudanar a shekara mai zuwa musamman idan aka yi la’akari manya-manyan wasannin da buga kungiyoyin kwallon daban-daban a duniya.

Dan wasan dai ya jima yana bada gudunmawa a lokuta daban-daban, kazalika rashin sa cikin tawagar ‘yan wasan Nijeriya (Super Eagles) ba karamin nakasu ba ne duba da gogewarsa da kuma yanayin yadda yake buga wasa daidai da yadda kasar ke bukata a halin yanzu.

Haka zalika, kwararren dan wasan yana daya daga cikin ‘yan wasan da ke jerin sahun gaba wajen lakanta da kuma fahimtar ita kanta kungiyar ta Super Eagles kwarai da gaske kuma suka san yadda kasar take buga wasa sosai. Saboda haka za mu iya cewa, Obi ya zama kusa a cikin tawagar ‘yan wasan kuma ya cancanci ya zama kyaftin na kungiyar.

Tun bayan bayyanarsa a cikin babbar tawagar ‘yan wasan Man city, Iheanacho ya samu kansa cikin wani yanayi sakamakon manyan ‘yan wasan gaba da suke bugawa Man city wasa.

Amma hakan bai sa dan wasan ya yi kasa a guiwa ba, domin da zarar ya samu dama yake zura kwallo a raga, kazalika yana taimakawa wajen zura kwallon a raga duk da karancin shekarun da yake da su.

Ya koma Manchester city ne sakamakon ci gaba da samun dammar buga wasa kuma indai yana samun wasanni a wannan shekarar tabbas idan aka je kasar Rasha zai taimakawa super eagles duba da irin basirarsa ta zura kwallaye a raga.

Kafatanin ‘yan wasan gaba na kungiyar Super Eagles, babu mai kwarewar Ighalo wajen zura kwallo a raga da takurawa ‘yan wasan baya na kungiyar hamayya.

Ya iya zura kwallo a raga kuma yana da gogewa ta buga manyan wasanni sakamakon zamansa a Watford ta kasar Ingila.

Idan har aka hada shi da Aled Iwobi a gaba, tabbas za a sha mamaki kuma kowanne a cikin su yana yawan zura kwallo a raga, sannan akwai kwallo a kafafunsu.

Kasancewar Ighalo a tawagar Nijeriya, ba karamin abu ba ne, kuma babu  shakka zai taimaka sosai musamman a manyan wasanni.

Yanzu dai abinda ake jira shi ne, sanin dawa-dawa za a tafi kasar ta Rasha, shin Gernot Rohr zai dauki ‘yan wasan da suka dace, ko kuma za a maimaita irin gidan jiya?

A gasar cin kofin duniyar da aka fafata a kasar Brazil a shekara ta 2014, Ahmad Musa ya samu nasarar zura kwallaye daidai har guda biyu a ragar Argentina a wasan rukuni-rukuni wanda Nijeriya tasha kashi a hannun Argentina da ci 3-2.

Musa, shararre kuma kwararren dan wasa wanda ya bugawa kasar nan wasanni daban-daban ciki har da gasar cin kofin duniya da kuma na Nahiyar Afrika. Wadannan dalilai ke nuna cewa ko shakka babu wannan hazikin dan wasa, zai taimakawa tawagar kugiyar kwallon kafa ta Super Eagles a kasar da ake sa ran farawa a shekara mai zuwa da za a gudanar a Rasha.

Kwararren dan wasan ya buga wa kungiyar kwallon kafa ta CSKA Moscow, ya kuma buga gasar zakarun Turai, sannan ya taba zama dan wasan da ya fi kafatanin sauran ‘yan wasa zura kwallo a raga a kofin kalubale na kasar ta Rasha.

Duk da cewa baya buga wasa a kungiyarsa ta Leceister city, amma zai taimakawa kungiyar Super Eagles matuka gaya sakamakon kwararrun ‘yan wasan suna taimakawa musamman a gasar cin kofin duniya.

“Kwararren dan wasa ne kuma zai taimaka min a gasar cin kofin duniya, saboda haka yana da amfani a wajena kuma ina fatan tafiya da shi zuwa kasar Rasha”. Wannan shi ne kalaman Gernot Rohr, mai horar da kugiyar Super eagles, bayan wasu masu sharhi sun soki kiran da ya yi wa Ahmad Musa a wasan da Nijeriya ta buga da Kamaru a watan Satumbar da ta gabata.

Babu shakka a halin yanzu za mu iya cewa shi ma Iwobi, karfinsa ya kawo don kuwa ko babu komai, zai taimaka kwarai da gaske wajen gasar cin kofin duniya idan muka yi la’akari da irin yadda yake buga kwallo a Arsenal da kuma ita kanta kasar ta Nijeriya.

Iwobi dan wasan gaba ne wanda ya kware wajen iya zura kwallo a raga, yake  kuma tayar wa da ‘yan wasan baya hankali da zarar ya samu kansa a cikin filin wasa.

Ya tsunduma cikin ‘yan wasan Arsenal ne a shekarar da ta gabata, ya  kuma nuna wa Mista Arsene Wenger cewa, ya cancanta ya rika bugawa Arsenal din kwallo.

A halin yanzu, kusan za mu iya cewa babu matashin dan wasa kamarsa a tawagar ta Super Eagles, kuma tuni masana suke ganin kamar zai iya taka muhimmiyar rawa a kasar ta Rasha, indai har Super Eagles din ta tafi da ‘yan wasan da za su taimaka masa wajen buga wasan.

Kamar yadda aka sani ne, Abdullahi shi ne wanda ya lashe kyautar dan wasa mafi hazaka da kokari cikin jerin ‘yan wasan Nijeriya da suka doke kasar Zambiya da ci 1-0, wanda wannan nasara ce ta kai Nijeriya ga samun gurbin zuwa gasar cin kofin ta duniya.

Ya kasance daya daga cikin ruhin ‘yan wasan baya na Super Eagles, sannan jigo a cikin ‘yan wasan musamman idan ana buga babban wasa ko kuma wata gasa ta daban.

Nijeriya ta jima ba ta yi dan wasan baya na bangaren dama kamar Abdullahi ba, kazalika magoya bayan Super Eagles, na matukar son ganin yana buga musu wasa, saboda kokari da kwazonsa na taimakawa ‘yan wasan baya, da na tsakiya a duk yayin da suke buga wasa.

Moses, na daya daga cikin kwararrun ‘yan wasan da muke da su a wannan kasa, yana kuma daya daga cikin ‘yan wasan da idan babu su a cikin jerin ‘yan wasan kwallon kafa ta Nijeriya sauran ‘yan wasan da muke da su ke shan wahala kwarai da gaske, saboda irin kokarinsa a wasa da kuma yadda yake iya zura kwallo a raga.

Ko shakka babu, dan wasa ne mai yi da zuciya kuma mai gudu da karfi wanda duk irin bayan da ya samu sai ya yi gaba da ita.Haka kuma yana da kwarewa ta buga manyan-manyan wasanni a tsawon zamansa a Chelsea.

Babu makawa ko shakku cewa, lallai wannan dan wasa zai buga abin a zo a gani indai har aka samu tafiya tare da shi kasar Rasha, ya kuma je a cikin koshin lafiya musamman ma idan yana kan ganiyarsa ta kokari.

Yana daya daga cikin ‘yan wasan da mai koyar da tawagar Super Eagles yake ji da su, yana kuma da yakinin cewa, indai har dan wasan zai je cikin koshin lafiya, tabbas za a sha mamaki.

Exit mobile version