Connect with us

WASANNI

‘Yan Wasan Nijeriya Uku Sun Ji Ciwo Kafin Wasar Ranar Asabar

Published

on

Hukumar kula da kwallon kwallon kafa ta kasa NFF ta bayyana cewa ‘yan wasan Super Eagles ta Nijeriya uku ne suka ji ciwo kuma ba za su buga wasan da kasar za ta fafata ba da kasar Sychelles a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Africa.

Hukumar ta bayyana haka ne a shafinta na yanar gizo inda ta ce, ‘yan wasan sun hada da Troost-Ekong da Aled Iwobi da kuma dan wasa Aina kuma nan gaba kadan za a sanar da wadanda za su maye gurbinsu.

Nijeriya dai za ta fafata wasa da tawagar kungiyar kwallon kafa ta Sychelles a can kasar bayan da suka buga wasan farko a nan Nijeriya da kasar Africa ta kudu suka yi rashin nasara har gida da ci 2-0.

Aina dai yaji ciwo ne a wasan da kungiyarsa ta Torino ta samu nasara da kungiyar SPAL a gasar Siriya A ta ranar Lahadi kuma aka maye gurbinsa da dan wasa Aled Berenguer a daidai minti na 86 da wasa.

Shi kuma Troost-Ekong ya samu ciwo ne a wasan da kungiyarsa ta Udinese ta sha kashi a hannun Fiorantina daci 1-0 duk da cewa ya gama buga wasan na minti 90 amma daga baya aka gano cewa ya ji ciwo.

Aled Iwobi bai buga wasan da kungiyarsa ta Arsenal ta samu nasara ba har gidan Cardiff  kuma ana zaton dan wasan zai dauki lokaci bai warke ba saboda tsananin ciwon.

A yau ne dai ake zaton kociyan kungiyar zai bayyana sunayen ‘yan wasan da zasu maye gurbin ‘yan wasan inda tuni daman kyaftin din tawagar, John Obi Mikel ya ji ciwo kuma ba a gayyace Shiba.

Advertisement

labarai