’Yan Wasan Roma Ba Za Su Sassautawa Salah Ba Idan An Je Italiya –Steven Gerard

Liverpool's Steven Gerrard smiles during his warm up before his team's English Premier League soccer match against Sunderland at Anfield in Liverpool, December 6, 2014. REUTERS/Phil Noble (BRITAIN - Tags: SPORT SOCCER) FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. EDITORIAL USE ONLY. NO USE WITH UNAUTHORIZED AUDIO, VIDEO, DATA, FIXTURE LISTS, CLUB/LEAGUE LOGOS OR 'LIVE' SERVICES. ONLINE IN-MATCH USE LIMITED TO 45 IMAGES, NO VIDEO EMULATION. NO USE IN BETTING, GAMES OR SINGLE CLUB/LEAGUE/PLAYER PUBLICATIONS.

Dan wasan Liverpool da tauraronsa ke hasakawa, Mohamed Salah zai fuskanci tsohuwar kungiyarsa wato Roma a matakin wasan dab da na karshe a wasa na biyu a gasar zakarun Turai, yayin  da tsohon dan wasan kungiyar Steven Gerard ke ganin cewa, dan wasan ba zai samu sassauci daga ‘yan wasan Roma a  fafatawar ta sati mai zuwa.

Salah ya zura kwallaye 34 a wasanni 83 da ya buga a lokacin da yake taka leda a Roma a gasar Siriya A kafin daga bisani ya koma Liverpool a kakar da ta gabata a kan farashin fam miliyan 34, yayin da ya ci wa Liberpool kwallaye 41 cikin wasanni 46 da ya guga ma ta.

A karon farko kenan da Salah dan asalin Masar zai kara da tsohuwar kungiyar tasa daya bugawa wasa shekara biyu

A karon farko  tun shekarar 2007, Liberpool na fatan kai wa matakin wasan karshe a gasar ta zakarun Turai, yayin da wasu ke ganin cewa, mawuyaci ne ba ta yi waje da Roma a gasar ta bana ba.

Sai dai kuma ita ma Roma na iya bada mamaki, musamman idan aka yi la’akari da rawar da ta taka wajen fitar da Barcelona daga wannan gasa a bana.

A gasar Europa kuma a yau ne Arsenal zata kara da kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid a filin wasa na Fly Emirates dake birnin Landan.

 

Exit mobile version