‘Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Southampton, wadanda su ka sha kashi da ci 9-0 a gida a hannun Leicester City ranar Juma’a “kwararrun ‘yan wasa ne”, in ji kociyan Manchester City Pep Guardiola.
Kungiyar zata fafata a filin wasa na Etihad a gasar Carabao Cup ranar Laraba ta kuma yi wasan Premier ranar Asabar, wasanninsu na farko tun bayan rashin nasara a hannun tsofaffin zakarun firimiya wato Leceister City.
Guardiola ya ce bazai yanke hukunci a kansu ba ko kuma ya shirya wasa tsakaninsa da su dangane da abin da ya faru da wasansu da Leicester ba saboda wasan kwallon kafa ne kuma sunyi iya kokarinsu.
‘Yan wasan Southampton da kuma masu horar da kungiyar sun riga sun bayar da wani tallafi ga mabukata sakamakon nasarar mai tarihi da suka samu karon farko tun bayan shekara 134 sia dai duk da haka, ana tsammanin masu horaswar biyu zasu gudanar da sauye-sauye da dama, kuma Guardiola yana tsammanin kyakkyawar manufa.
Guardiola ya ce ba abu ne mai sauki ba amma ‘yan wasan kungiyar kwararru ne kuma kociyan su zai yi bakin ciki na wani lokaci amma bayan hakan dole ne za su ci gaba da kara kaimi domin a cewar Guardiola sun san yadda kungiyar Leicester ta ke.
“Amma gasa ce daban-daban, misali Kofin Carabao da firimiya League kuma za mu yi kokarin mu kara shiri sosai don fuskantar kungiyoyi masu kyau saboda zasu fito ne kamar zaki mai jin yunwa saboda har yanzu sakamakon wasan Leceister yana zuciyarsu” in ji Guardiola
A wani labarin kuma, kyaftin din Southampton Pierre-Emile Hojbjerg ya ce wasan ranar Larabar wata dama ce ga ‘yan wasan su da su kara zage dantse a filin wasan domin nunawa magoya baya cewa tsautsayine abinda yafaru.