’Yan Wasan United Huɗu Zasu Sake Sabon Kwantaragi

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United zata ƙarawa wasu daga cikin yan wasanta guda hudu kwantaragi, domin ’yan wasan sucigaba da zama a ƙungiyar.

Uan wasan da zasu sake kwantaragin dai sun hada da Daley Blind dan ƙasar Holland da Ander Herrera na ƙasar sipaniya da takwaransa wato Juan Mata sai kuma Ashely Young dan ƙasar Ingila.

Dukkanin ’yan wasan dai watanni kadan yarage kwantaraginsu ya ƙare a ƙungiyar sai dai wataƙila ƙungiyar zata sake musu sabon kwantaragi domin cigaba da zama dasu.

Rahotannin sun bayyana cewa yan wasan zasu sake shekara dai-dai ne a ƙungiyar wanda zata kaisu har zuwa shekara ta 2019.

Ƙungiyar dai tana son fara tattaunawa da yan wasan ne da wuri kafin kwantaragin nasu yaƙare su fara tattaunawa da wasu ƙungiyoyin.

Shima dan wasan tsakiya na ƙungiyar, Maroune Fellaini saura shekara daya kwantaraginsa yaƙare sai dai rahotanni sunce tuni yafara tattaunawa da ƙungiyar domin sake sabon kwantaragi.

Exit mobile version