Yusuf Shuaibu" />

‘Yan Yahoo Sun Kai Wa Jami’an Tsaro Hari A Edo

A ranar Jumma’a mutane uku suka ji rauni a wani harin da ‘yan bindiga da masu bautar Amendo da kuma masu yaudarar intanet suka kai a Dagbala, a yankin Akoko-Edo na Jihar Edo.

Wani shaidar gani da ido, Mista Kehinde Libinus, ya ce shugaban rukunin kungiyoyin tsaro na yankin, Mista Steben Felid, ya ce an kai wa jami’an tsaro hari ne yayin da suke kokarin aiwatar da umarni zaman gida na gwamnatin jihar.

Ya ce sun je ne don tarwatsa taron masu bautar Amendo da wasu yara ‘yan Yahoo kafin lamarin ya rikice.

Libinus ya bayyana cewa jami’an tsaro uku sun samu raunuka a harin. Ya ce, “An garzaya da wadanda suka jikkata zuwa wani asibiti mai zaman kansa a Ososo don duba lafiyarsu. Ofayanmu yana bukatar Naira 150,000 don aiki amma jama’ar yankin za su iya samar da Naira 50,000 kawai.

“Shugaban gargajiya na yankin ya fada tun a farkon mako cewa ya kamata a hana duk wani sha’ani da suka shafi bukukuwan aure da duk taron jama’a don hana yaduwar kwayar cutar a ciki da kewayen Dagbala, kuma ya umarci masu taka tsantsan da su tabbatar da bin doka.”

Wakilinmu ya samu labarin cewa ‘yan sanda sun kama wasu mutane hudu da ke cikin Ososo dangane da lamarin.

Mun nemi jin ta bakin kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Mista Lawan Jimeta, da kakakin rundunar’ yan sanda, Mista Chidi Nwabuzor a kan lamarin amma abin ya ci tura saboda ba su dauki kiran waya ba, ko kuma amsar sakonnin da aka aika wa wayoyinsu.

 

Exit mobile version