Bello Hamza" />

Yana Da Kyau Matasa Su Rungumi Akidar Siyasar Zaman Lafiya -Maina

Shugaban matasa na jam’iyyar PDP ta kasa Alhaji Umar Babangida Maina, ya bayyana bukatar matasa a fadin ksar nan musamman matasan dake cikin jam’iyyar PDP dasu hada kansu su dunkuke domin fuskantar harkokin siyasan dake tafe, don kuwa daga dukkan alamu nasara na tare da jam’iyyar PDP.

Shugaban matasan ya yi wannan furucin ne a jawabin daya gabatar a taron hadin kai na (PDP NATIONAL UNITY MOBEMENT (NUM) da aka gudanar a garin Kastina ranar Asabar 21 ga wata Yuli 2018.

Shugaban matasan wanda shugaban kwamitin yakin neman zabe na ‘PDP at your Door Step forum’ Malam Ibrahim Dahiru Danfulani ya wakilta, ya kara da cewa,  kaddamar da kungiyar hadin  kai na jam’iyyar da aka yi ya zo a dai lokacin da ake bukata, “ Muna tsananin bukatar hadin kai don kawar da jam’iyyar APC mai mulki a halin yanzu.”

Ya ce, a ‘yan kwanakin nan, kashe kashe da ake yi a sassan kasar nan ya kazanta, kuma har yanzu gwamnati bata yi shirin gabatar da tsare tsaren da zai kare rayuwakan mutanen Nijeriya ba.

Muna da tabbacin cewa, duk wani shiri na ceto Nijeroya a halin yanzu dole sai an sa jam’iyyar PDP a ciki, soboda haka ya kamata dk dan ja’iyyar PDP ya jajirce wajen ganin ya bayar da gudummawarsa don a sami nasarar a zabukan dake tafe, inji shi.

Daga nan ya bukaci matasan jam’iyyar PDP dasu hada kansu suyi aiki tare don fuskatar guguwar siyasa dake dumfarrowa a halin yanzu.

Alhaji Babangida ya kuma yi bayanin cewa, shugabannin jam’iyyar karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar Prince Uche Secondus a wannan karon a shirye suke don tabbatar da bai wa kowa hakkinsa tare da tabbatar da dimokradiyya a wajen zaben dukkan ‘yan takarar da zasu tsaya wa jam’iyyar a zabukkan da za a yi, daga nan kuma ya yi kira ga dukkan ‘yan Nijeriya musamman wadanda basu karbi katin zabe ba dasu gaggauta yin haka “don sai dashi ne zamu iya tabbatar da burinmu na kawo canji yadda ya kamata”.

Daga karshe ya mika ta’aziyyarsa a bisa rasuwar tsohon shugaban rundunar ‘yan sanda Ibrahim Coomassie, Sardaunan Katsina da kuma mutum 52 da suka rasa rayukansu a ambaliyar ruwar data auku a jihar Katsina kwanakin baya, ya yi addu’ar Allah ya gafarta musu.

Exit mobile version