Connect with us

LABARAI

Yana Da Kyau Musulmi Su Koyi Da Karantarwar Ramadan –CAN

Published

on

An yi kira ga al’ummar musulmi da su yi riko da koyarwar addinin musulunci, domin addinin ne ya samar da azumtar Ramadan na kwanaki ashirin da tara zuwa talatin, in ko haka akwai karantarwar zaman lafiya da kaunar juna tsakanin mabambantan addinai. Shugaban kungiyar mabiya addinin kirista CAN reshen jihar Neja, Rebaran Dakta Mathias Echioda, ya yi kiran a lokacin da yake taya al’ummar musulmi kammala azumin Ramadan da bukin sallah karama a sakatariyar kungiyar da ke hanyar Dabid Mark a minna.
Mathias yace ya kamata musulmi su rungumi karantarwar Ramadan su yi riko da alheran da suka koya dan zaman lafiya da amana tsakanin su da ‘yan uwa mabiya addinin kirista, kasar ta mu daya ce, jihar nan na mu daya ne dan haka mu himmantu wajen samar da hanyoyin da za mu ciyar da ita gaba, domin dukkanin addinan nan suna nuni da zaman lafiya, hada hannu dan aiki tare ta yadda za a samu fahimtar juna.
Rebaran Echioda ya cigaba da cewar akwai wani mummunar dabi’a da ta shigo al’umma itace shaye shaye wanda dukkanin littafan addini ba inda aka koyar da shi, ya kamata musulmai a masallatai su tashi tsaye dan wayar da kan al’umma illar shi, haka su ma mabiya addinin kirista su tashi haikan a dakinan Ibadah su lurar da mabiya illarshi, aikin ba na gwamnati ne kawai ba Wajibin mu ne al’umma mu hada hannu dan ganin mun kawar da shaye shaye ga iyalan mu.
Shugaban ya yabawa gwamnatin jiha bisa namijin kokarinta na ganin ta inganta tsaro a cikin al’umma dan haka mabiya addinai su kara kaimi wajen yiwa gwamnatin addu’o’in samun nasara.

Advertisement

labarai