Yanayin Da Muka Bai Wa Makarantun ‘Tsangaya Model’ – Liman Kawo

Tsangaya

Daga Abdullahi Muhammad Sheka,

An bayyana kyakkyawan tsari da kuma yanayi mai kyau ya sa al’ummar Jihar Kano ke tururuwar kai yaransu mata irin makarantun ‘Tsangaya Model’ ta mata da maza da Gwamnatin Jihar Kano ta samar, domin kyautata tsarin koyi da koyarwar Alkur’ani mai girma.

Gwani Liman Kawo ne ya bayyana haka alokacin da Majalisar mahaddata Alkur’ani na Jihar Kano karkashin Jagorancin Goni Sunusi Abubakar suka ziyarci makarantun a makon da ya gabata.

Goni Sunusi Abubakar shugaban Majalisar mahaddata Alkur’ani na Jihar Kano da yake gabatar da takaitaccen jawabinsa lokacin da ya tsaya gaban daliban yana sauraron tilawar Alkur’ani da yaran ke rerawa, yace “dole ajinjinawa kokarin Hukumar Makarantun Allo da Islamiyyu na Jihar Kano karkashin Jagorancin Gwani Yahuza Gwani Dan Zarga. Yace lallai wadannan yara na samun kulawar data kamata kwarai da gaske.

Ya ce lallai wanda Bai san gari ba, to ya saurari daka, muna kara jinjinawa wannan Hukuma bisa wannan kyakkyawan tsari, sannan ya kuma yabawa kokari da jajircewar shugabar makarantar kwana ta tsangaya Model ta mata dake garin Tsakuwa, Hajiya Hadiza Adamu, we ya ce ko shakka babu tana rike da wadannan yara kamar ita ta haifesu.

Da ta ke jawabi ga tawagar Mahaddata Alkur’anin wadanda suka kai wannan ziyarar zumunci cewa tayi, babu shakka Allah ya amsa addu’ar da muka gabatar da yaran nan bayan idar da sallar asubahin wannan rana, inda muka roki Allah ya kawo mana bakin alhairi, kuma alhamdulillah sai ga tawagar Mahaddata Alkur’ani sun shigo mana.

Don haka ni da wadannan yara da abokan aiki na muna kara yiwa Allah godiya tare da rokon ahlullahi su saka mu cikin addu’o’i ako da yaushe domin samun nasara kan abububawan da Gwamnatin Jihar Kano Ke fatan ganin wadannan dalibai sun dace da samun ilimi gwargwadon iko. Tace kamar yadda kuke gani duk ranar Juma’a mukan umarci dalibai kowa ya yi kwalliya kamar suna gaban iyayensu, sannan sai mu shiga muyi salla tare ci gaba da tilawar Alkur’ani mai girma.

Gwanayen Alkur’ani da suke cikin tawagar data ziyarci wannan makaranatar Mata ta tsangaya Model dake garin Tsakuwa, sun jinjinawa himmar Hukumar dake lura da makarantun Allo da Islamiyyu ta Jihar Kano, inda suka yi alkawarin ci gaba sa wadannan dalibai cikin addu’o’i domin samun nasarar karatun da suke. Haka kuma sun jinjinawa shugabar makarantar Hajiya Hadiza Adamu wadda suka bayyana da cewa macece mai karkasashi da kaunar hidimtawa alkur’ani.

Exit mobile version