Muhammad Maitela" />

Yanayin da Wasu ‘Yan Mata SuKa Tsinci Kansu  Sansanin ‘Yan Hijira A Borno

Yau kuma za mu tabo wani bangaren na sakamakon halin ni’yasu da rikicin Boko Haram ya jefa wasu matasa, yan mata inda su ka tsinci kan su a zaman su na matsugunin yan gudun hijira a jihar Borno, al’amarin da ya canja rayuwar su tare da shiga wani sabon shafi na rayuwa, wanda ko a mafarki basu yi tsammanin sa ba.

Yagana (an sauya sunan yarinyar) yarinya ce yar kimanin shekara 14, wadda ke zaune a sansanin gudun hijira a jihar Borno. Yagana ta tsinci kan ta cikin mawuyacin halin ni’yasu; a lokacin da mayakan kungiyar Boko Haram suka taba sace ta daga garin su a wani mummunan hari da su ka kai, wanda sai bayan shekaru uku ta samu kanta- bayan sun yi mata fyade ba adadi.

Matashiyar, tayi sa’ar gudowa daga hannun mayakan, a daidai lokacin da suke bacci, al’amarin da ya jawo ta yi ta watan-garereniya a cikin dokar daji, daf da dajin Sambisa. Kwatsam, sai ga ta a sansanin yan gudun hijira, a matsayin wadda matsalar tsaro ta sauya wa rayuwa. Yagana ta ce, wata rana tana kwance a tantin su, sai ta ji motsin takon wani jami’n tsaro ya tunkaro ta wanda kan ka ce kwabo ya kutsa kai cikin tantin tare da cewa ta tashi ta fito waje- ba da wata gardama ba ta fito wajen.

Ta ce, sai ofisan ya dauke ta zuwa dakin sa tare da yi mata fyade. Ta ce, kuma bayan awa hudu da dawowar ta, sai ga wani ofisa shima ya zo, wajen ta wanda shima ya sake sungumar ta zuwa dakin sa tare da yi mata fyade.

Ta ce a wannan daren kadai, a haka wadannan jami’an tsaro suka yi ta sukuwa a kanta suna yi mata fyade; daya bayan daya, kuma ga halama wani bai san wani ya zo wajen ta ba.

Bugu da kari kuma, wata rana, cikin sulusainin dare Yagana ta farka daga bacci; bayan da ta tabbatar cewa kafa ta dauke a sansanin. Ta tashi a hankali; nan take sai ta ce, kafa me na ci ban baki ba, ta rinka gudu har Allah ya kai ta wani kauye wanda a nan ta ci karo da wata tsohuwa, wadda ta taimaka mata wajen nuna mata hanyar kubuta. Wanda a cikin wannan halin, sai ga jami’an tsaron soja, inda suka taimake ta wajen dauko ta zuwa matsugunin yan gudun hijira da ke birnin Maiduguri.

A haka Yagana ta tsira da ranta- duk da har yanzu ana iya cewa an gudu ba a tsira ba. Nan ma dai ta sake tsunduma cikin taskun tsohon turken ta mai cabo da ta guje wa. Duk da a wannan karon ta samu cikakkiyar kulawar wasu masu tausayi, ba kamar a baya ba.

Ta ce a matsayin ta na wadda ta gudo daga mayakan Boko Haram, babu ko sisin-kwabo kuma ba ta san inda zata ba, saboda bata san kowa ba a cikin birnin Maiduguri, kuma ga halama har yanzu tsugunne bai kare ba. Ta nemi a bata dama ta fita waje domin zuwa kasuwa- wajen masu kula da sansanin.

Sannan kuma a matsayin ta na karamar yarinya, ta tuna a baya kan cewa an taba zuwa da ita birnin Maiduguri sau daya, wajen kakarta, lamarin da ya jawo sai da jibin goshi ta gane unguwar. Bisa ga wannan masogarar ne sai Yagana ta nemi agajin wani ma’aikaci mai kula da sansanin yan hijira da ke tsaye a kofar shiga cikin sansanin.

Wanda nan take ta bayyana wa mutumin cewa don Allah ya taimake mata, ta shaida masa cewa wallahi tana cikin mawuyacin hali. Kuma tana jin tsaron kar mutanen nan su kashe ta. Wallahi kowane daren Allah sai sun zo waje ta.

Tausayin Yagana ya shiga zuciyar wannan mutumin, kuma nan take ya agaza mata inda ya bata kudin da za ta hau tasi domin gano unguwar da kakarta take. Haka kuma aka yi ta samu kakarta.

A baya, matsalolin fyade ga kananan yara ya zama ruwan dare tun bayan barkewar wannan rikici na Boko Haram, wanda ya shafi yankin arewa maso-gabashin Nijeriya a cikin shekaru 11 da suka gabata. Wanda a cikin wata kididigar da Majalisar Dinkin duniya ta bayar a shekarun baya ya nuna cewa, akalla manya da yara mata kimanin 7,000 ne aka sace tare da fuskantar irin wannan cin zarafi na fyade da dangogin sa a yankin.

Jaridar New-York Times (ta Amurka) ta ruwaito cewa a cikin wani binciken kwakwab wanda wakilin ta Adam Ferguson ya gudanar, ya zanta da yan mata 18 wadanda mayakan suka kama tare da yin amfani dasu wajen kai harin kunar bakin-wake.

Gefe guda kuma, an sha zargin wasu daga cikin jami’an tsaron Nijeriya wajen yiwa kananan yara mata fyade, da sunan bayar da kariya. Akwai gwamai na koke-koke da bincike ya gudanar na fyade da dangogin sa a cikin bakwai daga cikin sansanonin yan gudun hijirar Borno, wadanda ake zargin masu kula da matsugunan, jami’an tsaro tare da wasu yan sintiri na kato-da-gora. A binciken majalisar dinkin duniya ta tabbatar.

Exit mobile version