’Yancin Kai: Su Nijeriya Manya!

Sulaiman Bala Idris  isbdaurawa@gmail.com        

 Nmamdi Azikwe (daga 1-10-1963 zuwa 16-1-1966), Manjo Janar Johnson Aguiyi Ironsi (daga16-1-1966 zuwa 29-7-1966), Janar Yakubu Gowon (daga 1-8-1966 zuwa 29-7-1975), Janar Murtala Ramat Muhammad (daga 29-7-1975 zuwa 13-2-1976), Janar Olusegun Obasanjo (daga 13-2-1976 zuwa 1-10-1979), Alhaji Shehu Shagari (daga 1-10-1979 zuwa 31-12-1983), Janar Muhammadu Buhari (daga 31-12-1983 zuwa 27-8-1985), Janar Ibrahim Badamasi Babangida (daga 27-8-1985 zuwa 26-8-1993), Ernest Adegunle Oladeinde Shonekan (daga 26-10-1993 zuwa 17-11-1993), Janar Sani Abacha (daga 17-11-1993 zuwa 8-6-1997), Janar Abdussalam Abubakar (daga 8-6-1998 zuwa 29-5- 1999), Cif Olusegun Obasanjo (1999 zuwa 2007), Alhaji Umaru Musa ‘Yar’aduwa (2007 zuwa 2010), Dakta Goodluck Ebele Jonathan (2010 zuwa 2015), Muhammadu Buhari (2015 zuwa yau)

Kai Alhamdulillahi, ko wayyo Allah za mu ce?, lokaci kenan mai tafiya kamar kibiya, wai har mun shekara 57 da samun ‘yancin kai, ma’anar ‘yancin kai shi ne samun walwala da faraga ta morewa tattalin arzikin ƙasar mu yadda ya kamata. Sai dai kash! daga 1960 zuwa yau Allah ne kaɗai ya san irin halin da al’ummar Nijeriya suke ciki, Allah na ƙara wadata ƙasar wasu na wawurewa suna zura wa a aljihunan su.

Idan ka kalli zubin mutanen Nijeriya a yau, za ka fahimci irin nasarar da a ka samu, ka kalli kowanne mutum a ƙasar za ka ga ya na cikin ƙoshin lafiya, kwanciyar hankali da wadacciyar dukiya, ga kuma aikin yi da a ka yalwata al’umma da shi, yara duk an tura su makarantu domin su ilmance, matasa kuma sun bar tasha da ƙasan gada sun kama ayyukan yi. Zancen banza! ko a duniyar mafarki ma ƙarya ai an san harkar ƙurungus ce wannan.

Kowanne shugaba ya na da nasarar da ya haifar wa ƙasar kafin gushewarsa, amma ni ba zan bankaɗi nasarar kowa ba, sai wacce Obasanjo ya fara assasawa, domin daga kansa ne a ka dawo da mulkin farar hula ƙarƙashin tutar dimokraɗiyya, bayan rasuwar Janar Abacha, tarihin baya duk komatsen tatsuniya ce, idan ma Nijeriya za ta samu wani nasara ya kamata a fi bayar da ƙarfin tsammanin nasarar daga 1999 zuwa yau, saboda Allah ya koro duk wata albarkar shi ga tattalin arzikin ƙasar, ya kuma bunƙasa wadatar komai, amma duk da haka harkar ‘Mai Ƙarfi Ya Tsira’ ake gwada wa talaka.

Kamata ma ya yi a sanya wata doka ta garƙame duk wani wanda ya ce Obasanjo bai kawo ci gaba ga ƙasar nan ba, nasarar da ya kawo, sai dai mu bar shi da Allah ya saka mishi kawai, domin ba mu da wata lada da za mu biya shi da ita, illa a bar wa Allah, idan an haɗu ranar sakamako sai kowa ya sha kallo. Ga kaɗan daga wasu abubuwa na ci gaba da Obasanjo ya wadata Nijeriya da su kamar haka:

A lokacin mulkin Obasanjo ne a ka samu yawaitar kashe-kashen al’umma, misali rikicin ƙabilancin da ya addabi mutane a sassa daban-daban, a tarihin Nijeriya lokacin mulkin Olu ne irin wannan rikici ya fi ƙazanta, an yi rikicin Hausawa da Yarbawa a Legas, an yi rikici tsakanin Jukun da Tiɓi, an kuma yi rikicin ƙwacewa Fulani Mata a Shendam ta Jihar Filato. Nasarar farko da Obasanjo ya fara samu kenan na tarwatsa kan al’umma.

Obasanjo ya tsiyata mutanen Nijeriya sosai, masu gidan kansu sun siyar sun kama haya, me ka ji ko ka sa-ni game da gidajen IKOYI inda Obasanjo ya fito fili ya ce duk wani ɗan uwansa, da matansa na aure (Waɗanda ba a san adadinsu ba), da karuwansa (ciki har da matar ɗansa wacce suka yi taraliya da ɗan nashi a gaban kuliya), wai har da karnukansu, duk sun sami kyautar gidaje a muhallin. Ka ga wannan ma ba ƙaramin nasara ba ne ya samu, domin ya talauta miliyoyi ya wadata iyalansa, karuwansa da karnukansu.

Da gangan kuma ya na sane Obasanjo ya ɗauko marigayi ‘Yar’aduwa a matsayin magajinshi, saboda ya san marigayin ba shi da wadatacciyar lafiyar da zai iya gudanar da al’amura yadda su ka dace.

Wasu shahararrun Katsinawa ne kawai suka ci ribar kasantuwar ’Yar’aduwa Shugaban ƙasa, saboda su ne su ka riƙa sace–sace a ma’aikatun tarayya. Wasunsu tun bayan da ’Yar’aduwa ya rasu ɓerayen suka yi gum, wasu kuma suka ranci na kare don tsoron EFCC.

Haƙar Obasanjo ta cimma ruwa, domin babu wani abu da marigayi Umaru ya iya cimma har rai yayi halinshi. Sai mataimakinshi Goodluck ya ci moriyar kujerar shugabancin ƙasar.

Me gwamnatin Goodluck ta yi?. sunan wani abu kwashi-kwaraf, kawai an ci gaba da kashe–kashen ba gaira-ba-dalili ne. Rayuka sun salwanta da sunan Boko haram, an yi wa ’yan mata fyaɗe son rai, a garuruwan Maiduguri, da Yobe duk da sunan tabbatar da tsaro.

Gwamnatin su Goodluck ta yi ƙaurin suna a matsayin gwamnatin ‘yan taurin kai da rintse ido. Duk cikin taurin kan ne ya sa a lokacin Goodluck ya yi biris da koken malaman jama’a, sannan kuma gwamnati ce ta waɗanda ba su iya magana ba. Irin ɓaƙaƙen kalaman da tsohon shugaban ƙasa Goodluck da muƙarrabansa su ke faɗa wa malaman Jami’a kaɗai ya isa a fahimci haka. Kisa da sunan siyasa ya yawaita, sai ka ga an kashe mutum wai don bai yi imani da ra’ayin wani ba, a na iya halaka unguwa guda saboda wata manufa, rayukan Karnuka, Maguna, Kiyashi, duk sun fi ran mutum daraja a Nijeriyar zamanin mulkin Goodluck, wannan duk rashin imanin da ke zukatan shugabanninmu ya jawo mana, ba ka jin ɗuriyar kowa sai Alhaji, ko Sarki, ko Manaja, ko Darakta, ko Yallaɓai da ire – irensu.

Ita ma dai wannan gwamnatin mai ci, ta Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wacce saboda shaharar ta, sai da talakawa suka yi ta mutuwa yayin murnar lashe zaɓensa. Me ya biyo baya? Talauci, fatara, da rashin daidaituwar lamurra.

A fanni guda, za a iya cewa gwamnatin Buhari ta yi ƙoƙari, an daina fashe-fashen nakiya a kasuwanni, makarantu da ofisoshin jami’an tsaro. Sannan kuma ɓarayin gwamnati na fargabar yin watanda da dukiyar da ba ta gadon gidansu ba.

Talauci kuwa, kai ka ce ita wannan gwamnatin me ci, abin da ta zo gadar wa da al’umma kenan. Duk wanda ka jima ba ku haɗu ba, da zaran ka ganshi, sai dai ka ganshi da rafkeken kai, da ɗan mitsitsin jiki, yunwa ta ci shi ta cinye. Ga kuma rikicin kurayen cikin gidan APC sun hana komi tafiya ballantana ma a yi wa talakawa aikin da ya dace da su. Hmm! Barka da Zagayowar shekara ta 57 da samun ’yancin kai kawai zan ce.

Exit mobile version