Wani mutum dan shekaru 49, mai suna Wada Haruna, wanda ya amsa laifin yiwa yarinya ’yar shekaru 12 fyade a garin Jos hukuncin shekaru hudu a gidan yari.
Wata babbar kotu a garin Jos wacce take da matsuguni a Kasuwar Nama ce ta yanke wannan hukunci. Kotun ta bayyana cewa wanda ake zargi da laifi ya amsa laifinsa, ba tare da wahalar da shari’a ba.
Alkalin, Mista Yahaya Mohammed, ya bayyana cewa tunda wanda ake zargi ya amsa laifinsa akan zargin da ake yi masa, kotun ba ta da wani zabi banda ta hukunta shi.
Mohammed ya ce, wannan hukuncin zai zama darasi ga duk wani mai irin wannan hali, ko mai tunanin aikata irin wannan danyen aiki.