Jami’an ‘yansanda da ke Abuja sun samu nasarar kame wasu mutum goma sha tara, da ake zarginsu da laifin garkuwa da mutane, da kisan kai da kuma wasu miyagun ayyuka. Kwamishinan ‘yansanda na Birnin tarayya, Abuja, Babaji Sunday, ya ce, mutum uku daga cikin wadanda aka Kaman ana zarginsu da laifin kashe Dakta Obisike Donald Ibe, mai kimanin shekara 37 wanda ke aiki a cibiyar binciken koda ta Zenith Lab, da abokinsa da wani abokin zamansa, Ezekiel Edoja dukkansu suna zaune a rukunin gidaje na Games da ke Abuja.
Wadanda ake zargi da aikata wannan laifi su ne, Abdulsalam Ibrahim da da Fidelis Ezekiel da Phillimon Hussaini. Wadanda ake zargin sun tabbatar da aikata wannan laifi, lokacin da ake bincikensu.
Kwamishinan ya ce, tun da suka samu wannan rahoton suka dauko gawarwakin kuma suka ci gaba da farautar wanda ya yi wannan danyen aiki.
Wanda ya aikata wannan aiki kuma ya gudu da wata mota da kuma wasu kudi kimanin dala 1,000, da wayar wannan likita da katin ATM. Kwamishinan ya ce, a cikin watan Janairu sun samu rahoto daga ofishinsu na Karu kan kashe wani manomi mai suna Mohammed Usman. Binciken da ‘yansanda suka yi, ya sa suka kama, Muhammed Abubakar, wanda kuma da kansa ya yi bayani a rubuce, cewa, shi ne, ya dabawa marigayin wuka kuma ya gudu, bayan wata sa-in[1]sa tsakaninsa da Daktan, sakamakon haka kuma ya mutu.
Haka kuma, a cikin watan Janairu ‘yansanda sun kama Shu’aib Usman da Sani Auwal. Sauran wadanda ake zargin su ne, Sani Auwal, wanda ake zarginsa da sa hannu wajen yin garkuwa, da kuma yunkurin koyawa wasu yadda za su yi garkuwa. Yanzu haka Auwal na tsare a hannun ‘yansanda, suna ci gaba da bincikensa.