‘Yansanda sun kama mutane takwas da ake zargi da kisan wani jariri da kuma birne shi a Asibitin Kwatam da ke kan titin Baga da ke Maiduguri, a Jihar Borno.
Lamarin ya faru ne ranar Juma’a, 18 ga watan Afrilu, 2025, da misalin ƙarfe 1 na rana, bayan da wasu mazauna yankin suka hango wasu mutane na ƙoƙarin birne jaririn a cikin harabar asibitin, suka kuma sanar da ‘yansanda.
- Shin Ziyarar Bazata Zuwa Gidan Budurwa Daga Saurayi Na Bata Wa ‘Yanmatan Rai?
- Wayar Da Kai Kan Barazanar Intanet A Rayuwar Al’umma (CYBER AWARENESS)
Jami’an tsaro sun garzaya wajen tare da mamaye yankin, suka kuma kama waɗanda ake zargin.
Daga baya masu bincike sun tono gawar jaririn domin gudanar da bincike.
Yanzu haka, an miƙa waɗanda ake zargin ga Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) domin ci gaba da bincike kan lamarin.