Connect with us

WASANNI

Yanzu Ba Ma Neman Modric — Inter Millan

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Inter Millan ta bakin daraktan wasanni na kungiyar Pabio Aurelio ta bayyana cewa kungiyar tasu yanzu bata bukatar dan wasan tsakiyar Real Madrid Luca Modric domin sunada ‘yan wasan da zasuyi amfani dasu.
A kwanakin baya dai an danganta dan wasa Modric da komawa Inter Millan tun bayan dawowarsa daga gasar cin kofin duniya sai dai dan wasan ya bayyana cewa zancen babu gaskiya aciki kuma yana farin ciki a kungiyarsa.
Kungiyar kwallon kafa ta Inter Millan dai tana neman dan wasan tsakiya mai irin shekarun Modric domin kalubalantar kungiyar kwallon kafa ta Jubentus wajen neman lashe gasar Siriya A da kuma buga gasar zakarun turai.
“Mun hakura da neman dan wasa Modric saboda ‘yan wasanmu da muke dasu yanzu sun ishemu kuma dasu zamu buga kakar wasa sai dai muna karancin kwararrun ‘yan wasa da kuma ‘yan wasan benci amma a haka zamu tafi” in ji daraktan wasannin na kungiyar
Yaci gaba da cewa “Akwai manyan ‘yan wasan da zamu tafi dasu sannan kuma munada kwararru da matasan ‘yan wasa wadanda zasu kaimu duk inda mukeso idan har suka cigaba da buga wasa yadda yakamata”
Sannan a karshe ya bayyana cewa a shirye suke dasu siyar da dan wasan kasar Portugal, Jao Mario wanda yakeson barin kungiyar inda yace tuni suka saka dan wasan a kasuwa ga duk kungiyar da takeson siya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: