Ga dukkan alamu dai ta faru ta kare game da tsame wasu jami’an gwamnatin Buhari da aka nada a mukamai daban-daban a cikin umarnin murabus ga duk mai son tsayawa takara a 2023, da Shugaba Buhari ya bayar a jiya Laraba.
Da safiyar yau Alhamis Buhari ya fitar da wata sanarwar cewa duk wani nadadden jami’in gwamnati da ke shugabantar ma’aikata ko hukuma da yake muradin takara ya yi murabus.
- 2023: Duk Wanda Ya Yanki Fom Din Shiga Takara Ya Ajiye Mukaminsa —Buhari
- 2023: Minista Ya Yi Murabus Jim-Kadan Bayan Umarnin Da Buhari Ya Bayar
- 2023: Zan Shawarci Buhari Da ‘Yan Mazabata Kafin Na Yi Murabus —Ngige
Babban Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya rattaba wa sanarwar hannu wacce LEADERSHIP ta samu kwafinta.
Sanarwar an aike ta ga dukkan ministoci, shugabannin ma’aikatu na tarayya, babban mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaron kasa, shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), shugaban Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa ta ICPC, Shugaban Hukumar Yaki Da Damfara Da Kassara Tattalin Arzikin Kasa (EFCC) da sauransu.
Sanarwar ta ce dukkan wani mai son takara da ke kan kujerar shugabanci ta nadi ya yi murabus kafin nan da ranar Litinin 16 ga Mayun 2022.
“Domin kawar da duk wata tantama, wannan umarni ya shafi dukkan ministoci, shugabannin hukumomin gwamnati, jakadu da sauran wadanda aka naɗa a mukamai na siyasa da suke da muradin tsayawa takara.
“Domin ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati yadda ya kamata, dukkan ministocin da abin ya shafa za su mika ragama ga kananan ministocin da ke ma’aikatunsu, idan kuma babu karamin minista a ma’aikatar, su mika ga manyan sakatarorin ma’aikatun.
“Su kuwa jakadodi su mika ragama ga mataimakansu ko kuma babban jami’i da ke ofishin jakadancinsu kamar dai yadda yake a ka’ida.” In ji sanarwar.
Tuni dai tun jiya Laraba wasu ministocin suka yi murabus bayan samun umarnin na Shugaba Buhari.