Connect with us

WASANNI

Yanzu Duniya Za Ta San Har Yanzu Ronaldo Yana Nan –Zidane

Published

on

Tsohon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Zinedine Zidane ya bayyana cewa yanzu duniya za ta san cewa har yanzu Ronaldo yana kan ganiyarsa tunda ya fara zura kwallo a raga a sabuwar kungiyarsa.

Christiano Ronaldo ya jefa kwallayensa na farko a raga tun bayan da ya koma Jubentus don ci gaba da buga wasa daga kungiyar Real Madrid akan kudi kusan fam miliyan 105.

Dan wasan ya zura kwallaye biyu a fafatawar da Jubentus ta doke kungiyar Sassuolo da ci 2-1 a gasar Seria A bayan da ya buga wa kungiyar tasa wasanni uku ba tare da jefa kwallo ba.

Sai dai tsohon kociyan na Real Madrid kuma tsohon dan wasa Jubentus din ya bayyana cewa yanzu dan wasan hankalinsa zai kwanta kuma zai san cewa kungiyar Jubentus akwai dadi musamman idan kana babban dan wasa.

Kiris ya rage dan wasan mai shekaru 33 ya jefa kwallaye fiye da biyu a fafatawar ta jiya, lura da cewa ya barar da damammakin zura kwallo har guda biyu da ya samu.

A bangare guda, alkalin wasa ya kori dan wasan Jubentus, Douglas Costa, dan kasar Brazil bayan fasahar bidiyon da ke taimakawa alakalin wasa ta nuna shi yana tofa wa dan wasan Sassoulo, Federico di Francesco yawu bayan takaddamar karbe kwallo da ta kaure a tsakaninsu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: