Yanzu Hankalina Zai Dan Kwanta, Inji Conte

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Mai koyar da yan wasan kungiyar Chelsea Antonio Conte ya ce ya kasa barci a ‘yan kwanakin nan saboda wasan da kungiyarsa za ta yi na matakin kungiyoyi 16 na zakarun Turai da Barcelona a Stamford Bridge sai dai yanzu hankalinsa zai kwanta bayan buga wasan na farko.

Ya ce a kwanakin nan bayan wasan da aka fitar da su daga gasar kofin FA, tun daga wannan lokacin ya kasa samun barci da kyau.

Conte ya ce ya samu kansa cikin wannan yanayi ne saboda zai fuskanci kungiyar da take daya daga cikin fitattun gwanaye na duniya, kuma wadanda ma ake kallon za su dauki kofin na Turai.

Barcelona na kan hanyarta ta cin kofuna uku ne a bana kuma kawo yanzu ba a doke su ba a gasar La Liga, wadda suke kan gaba da tazarar maki bakwai.

Sai dai kuma kociyan dan kasar Italiya ya ce, a daya bangaren suna murna da hakan saboda wata dama ce a wurinsu ta su tashi tsaye su nuna iyawarsu a kan wannan babbar kungiya, kuma su nuna matsayinsu.

Chelsea dai ta ci hudu ne kawai daga cikin wasanninta 12 da ta yi a karshen nan wanda hakan yaja cece kucen cewa watakila kungiyar ta sallami Conte a yan kwanakin nan.

Kungiyar ta yi rashin nasara a hannun Arsenal a wasansu na kusa da karshe na cin kofin Carabao (EFL) a watan Janairu, sannan kuma ta sha kashi a gasar firimiya a hannun Bournemouth da Watford.

Sai dai kuma kungiyar ta fara farfadowa inda ta yi nasara a kan West Brom a gasar firimiya ranar 12 ga watan Fabrairu, ta kuma biyo baya da doke Hull City, a wasan cin kofin FA zagaye na biyar ranar Juma’a.

Ana dai ta muhawara a kan makomar Antonio Conte a kungiyar ta Chelsea a bana, kuma bayan wasan nasu da Barcelona zai fuskanci wata babbar karawar da Manchester United a wasan firimiya ranar Lahadi a filin wasa na Old Trafford.

 

Exit mobile version