Yanzu Karfin Mu Ya Dawo, In Ji Wenger

Mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger, ya bayyana cewa zuwa yanzu karfin kungiyar ya dawo kuma zasu iya doke kowacce kungiya a kakar wasannan da ake bugawa.

Arsenal ta yi nasarar cin kungiyar Everton kwallo 5-1 a gasar firimiya wasan mako na 26 da suka fafata a ranar Asabar a filin wasa na Fly Emirates dake birnin Landan.

Tun kafin aje hutun rabin lokacine Arsenal ta ci kwallo hudu ta hannun Ramsey da ya ci biyu da wadda  dan wasan baya, Laurent Koscielny ya ci, sannan sabon dan wasan da Arsenal din ta siyo, Aubameyang ya ci ta hudu.

Bayan da aka dawo ne daga hutu Calbert-Lewin ya ci wa Ebrton kwallonta daya tilo, daga baya Ramsey ya ci ta biyar kuma ta uku a fafatawar.

Da wannan sakamakon Arsenal ta ci Everton kwallo sama da 100, kuma babu wata kungiya da Arsenal ke yi wa ruwan kwallaye kamar Eberton.

Kocin Everton, Sam Allardyce ya ja ragamar wasan firimiya na 500 a kungiyoyin da ya horar, kuma shi ne na biyar da ya taka wannan tsanin na adadin wasanni 500 din.

Arsene Wenger ya ci wasanni guda 500 a firimiya, yayin da Harry Rednaff ya yi canjaras, shi kuwa Dabid Moyes da Sir Aled Ferguson kashi suka sha.

Exit mobile version