Yanzu Manchester United Ce Kawai Nake Son Karyawa Wuya – Guardiola

Guardiola

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola, ya bayyana cewa, bayan nasarar da kungiyarsa ta samu akan kungiyar Wolberhampton a ranar Talata yanzu hankalinsa ya karkata zuwa yadda zai buga wasa da Manchester United a wasan hamayyar da za su fafata a ranar Lahadi.

Manchester City ta ci gaba da jan ragamar teburin Premier League, bayan da ta doke Wolberhampton da ci 4-1 a filin wasanta na Etihad ranar Talata kuma hakan ya kawo nasara ta 21 kenan a jere.

Minti 15 da fara wasan Wolbes ta ci gida ta hannun Leander Dendoncker, yayin da Conor Coady ya farke bayan da suka koma karawar zagaye na biyu, bayan hutu kenan sai dai Manchester City ta kara ta biyu ta hannun dan wasanta na gaba Gabriel Jesus, sai Riyad Mahrez ya kara ta uku, sanan Gebriel Jesus ya ci ta hudu kuma ta biyu a fafatawar.

Da wannan sakamakon Manchester City ta ci wasa 21 a jere a dukkan fafatawa , kuma na 28 da ba a samu nasara a kanta ba wanda hakan yasa yanzu babu wanda yake da irin wannan tarihin a Ingila.

Rabon da a yi nasara a kan Manchester City tun ranar 21 ga watan Nuwamba, wanda Tottenham ta doke kungiyar ta Etihad da ci 2-0 a gasar Premier League sannan tawagar ta Guardiola ta ci wasa 21 a jere tun bayan da ta tashi kunnen doki 1-1 da West Brom ranar 18 ga watan Disamba.

A wasa 21 da ta ci a jere har da karawa biyu a Caraboa da uku a FA Cup da cin wasan Champions League daya, sauran bajintar a Premier League ta yi sannan Manchester City ta ci gaba da zama ta daya a kan teburi.

“Bayan mun kammala samun nasara a wasan Wolbes na gayawa ‘yan wasa na cewa yanzu sai mu mayar da hankali akan wasan da zamun karbi bakuncin Manchester United a wasan da zamu fafata ranar Lahadi kuma tuni na fara shirin yadda zamu tunkari wasan” in ji Guardiola

Ya kara da cewa “Babban abinda yake gabana yanzu shine ganin mun samu nasara a wasan saboda kowa yasan wasan hamayya ne kuma Manchester United ba karamar kungiya bace a duniya”

Ya ci gaba da cewa “Ina fatan samun nasara a wasannin mu da suka rage gaba daya saboda haka idan muka mayar da hankali akan abinda yake gaban mu tabbas zamu bawa duniya mamaki ta hanyar lashe wasannin mu gaba daya”

Kungiyar ta Etihad mai fatan lashe kofi hudu a bana ta kai wasan karshe a gasar cin kofin Carabao Cup da Kuarter finals a FA ta kuma ci Gladbach a Champions League, ita ce ta daya a Premier.

 

Exit mobile version