Abba Ibrahim Wada" />

Yanzu Ni Ne A Gaba Da Messi, Cewar Van Dijk

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Virgil Van Dijk, ya soki dan wasan gaba na Barcelona, Leonel Messi, inda yace yaje ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya tunda shi ya lashe kofin zakarun turai.

Tun bayan komawarsa Liverpool Van Dijk ya kasance jigo a tafiyar kungiyar inda ya mayar da Liverpool kungiyar da ake shayi a duniya bayan da tun farko kungiyar ake ganin tanada matsala musamman a bangaren baya.

Wannan kokarin kuma ya ja Liverpool ta lashe kofin na zakarun turai karo na shida sannan kuma suka buga wasanni shida ba tare da an zura musu kwallo  a raga ba a gasar wanda hakan yasa ake ganin duk yana daya daga cikin kokarin dan wasan bayan.

“Ina tunanin duk duniya babu kamar Messi saboda haka yaje ya lashe gasar Ballon “d”Or ni kuma na lashe kofin zakarun turai saboda ya cancanta ya lashe kyautar duba da irin kokarin da yayi a gasar amma dai yanzu nine a gaba dashi”.

Dan wasan bayan dan kasar Holland ya cigaba da cewa “Bana tunanin zan iya lashe kyautar amma kuma Messi zai iya lashewa kuma wannan kofin dana dauka a yanzu yafi waccan kyautar da zai lashe”

Bayan ya lashe kyautar gwarzon dan wasan firimiya na bana wasu suna ganin shahararren dan wasan bayan zai iya kasancewa dan wasa na biyu bayan Fabio Cannavaro na kasar Italiya wajen lashe kyautar ta gwarzon dan wasan duniya bayan dan kasar Italiyan ya lashe kyautar a shekara ta 2006 bayan kammala gasar cin kofin duniyar da Italiya ta lashe a kasar Jamus.

Exit mobile version