Connect with us

Da dimi-diminsa

Yanzu-yanzu: Allah Ya Yi Wa Sarkin Rano Rasuwa

Published

on

LEADERSHIP A YAU Ta tabbatar da samun rahoton rasuwar Sarkin Rano ta Jihar Kano, Alhaji Tafida Abubakar Ila Na 2, Autan Bawo. Sarkin ya rasu ne da yammacin yau Asabar bayan wata ‘yar gajeruwar rashin lafiya. Da safiyar yau aka ce an garzaya da shi asibiti, inda dazu da yamma aka sanar da rasuwarshi.

Sarkin na Rano yana daga cikin sabbin masarautun jihar Kano da gwamnatin Jihar karkashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta samar a kwanakin baya, inda aka dinga dambarwar siyasa wacce ta kai ga tsige Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na 2.

Ba a kai ga sanar da lokacin da za a yi mishi Jana’iza ba. A kasance tare da mu don samun cikakkun labarai.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: