Yanzu-yanzu: Matasa Sun Fara Kone-kone Sakamakon Harbe Direba A Gashuwa

Daga Muhammad Maitela Damaturu,

Biyo bayan zargin sojoji da harbe wani direba, Muhammad (Tooli) Musa a lokacin da yake kokarin shan mai a motarsa a gidan man ‘Yamaco’ da ke Garin Alkali da ke yankin karamar hukumar Bursari a jihar Yobe da yammacin ranar Jummu’a.

Hakan ya jawo kungiyar motocin Sufuri ta kasa (NURTW) reshen jihar Yobe daukar matakin hana zirga-zurgar ababen hawa a garin Gashuwa har sai an gudanar da binciken abin da ya jawo halaka direban wanda su ke zargin sojoji da aikata wa.

daya daga cikin jami’an hukumar NURTW a jihar wanda bai yarda na nadi muryar sa ba, ya ce, “Mu na zargin sojoji ne da kisan Muhammad Musa (Tolli) ba tare da wata hujja ba. Kuma mun dauki wannan matakin domin nema masa hakkinsa, sannan yanzu haka da muke magana da kai mun yi magana da Kwamandan sojojin Gaidam kan lamarin kuma ya tabbatar mana cewa mu jira zuwan sa nan da 9:00 na safe.”

Bugu da kari, bisa haka ne dubban matasa a garin na Gashuwa su ka hau titunan garin suna kone-kone tare da zanga-zangar nuna rashin jin dadin wannan aika-aika wadda suke zargin sojojin da aikata wa. “Mun fito wannan zanga-zangar ne don bayyana bacin ranmu dangane da kashe abokinmu- Muhammad Tolli, ba tare da aikata laifin komai ba.” Ta bakin masu tarzilomar.

Ku biyo mu don cikakken rahoton….

Exit mobile version