A ranar Laraba ne hukumar shirya jarabawar kammala sakandare ta Afirka ta Yamma (WAEC), ta sanar da cewa ta rufe shafin intanet dinta na duba sakamakon jarabawa na wani dan lokaci sakamakon wasu matsalolin na’ura kadan bayan ta fitar da sakamakon WASSCE na shekarar 2025.
WAEC ta sanar da hakan ne a shafinta na X (Twitter)
A halin da ake ciki, WAEC ba ta bayyana ainihin abin da ya faru ba don gane da matsalar ba amma ta tabbatar wa jama’a cewa ana kokarin shawo kan matsalar.