Connect with us

WASANNI

Yanzu Za A Fara Ganin Amfanin Ronaldo A Real Madrid

Published

on

Tsohon dan wasan kungiyar Real Madrid Guti, ya bayyana cewa yanzu kungiyar za ta fara tabbatar da cewa ta yi kuskure da ta siyar da dan wasa Cristiano Ronaldo a wannan shekarar

Cikin wani yanayi na bazata, Real Madrid tasha kashi da kwallaye 3-0, a wasan gasar La liga da ta fafata da kungiyar Sebilla a ranar Larabar da ta gabata a wasan sati na biyar na gasar.

Karo na farko kenan tun bayan shekarar 2003, da Real Madrid ta fuskanci irin wannan kaye na jefa mata kwallaye 3 kafin tafiya hutun rabin lokaci, a waccan lokacin shi ma kayen a hannun kungiyar ta Sebilla ne.

Wasan na ranar Laraba dai dama ce ga Real Madrid wajen darewa saman teburin gasar La liga, la’akari da rashin nasarar abokiyar hamayyarta wato Barcelona, wadda kungiyar Leganes ta shammace ta samu nasara a kanta da kwallaye 2-1.

“Yanzu maganar da muka fada tun farko za ta fara fitowa fili tunda daman mun bayyana cewa kada kungiyar ta kuskura ta sayar da Ronaldo a wannan yanayin, saboda maye gurbinsa abu ne mai matukar wahala” in ji Guti

Ya ci gaba da cewa “Ronaldo dan wasa ne wanda idan yana cikin fili kowacce kungiya take jin tsoronsa, saboda a ko da yaushe yana iya zura kwallo a raga kuma yana da tasiri a wasa ko da a ce bai ci kwallo ba”

Har yanzu dai Barcelona ce ke jagorantar gasar ta La liga da maki 13, yayin da Real Madrid ke biye mata, ita ma da maki 13, sai kuma Atletico Madrid da maki 11 a matsayi na uku.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: