’Yar Aiki Ta Sace Miliyan 1.6 Bayan Awa Shida Da Daukar Ta Aiki

Tawagar rundunar ‘yan sanda sun damke wata ‘yar aikin gida mai suna Franker Amaha ‘yar shekara 26, bisa laifin satar kudi har na naira miliyan 1.6, daga wajen uwar gidanta, bayan awa shida da daukar ta aiki. Wacce a ke zargin ‘yar asalin Jihar Koros Ribas ce, inda Misis Taiye ta dauke ta aikin gida a yankin Masha cikin Surulere ta Jihar Legas. Awanni biyu da daukar ta aiki, sai uwar gidanta ta tura Amaha filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Ikeja, domin ta dauko ‘yar’uwarta wacce ta tafi kasar waje. Ta na dawowa gidan, sai Amaha ta shiga dakin da ‘yar’uwar matar ta ijiye kayayyakinta, sannan ta sace dala 2,800 da fam 1000 kudin kasar Ingila tare wasu kayayyaki, sai ta gudu daga cikin gidan.

Wannan lamari dai ya faru ne cikin awa shida da daukar Amaha aiki a gidan, inda ta bar uwar gidanta da ‘yar’uwarta cikin rudani. Sun dai kai rahoton faruwar lamarin ga ofishin ‘yan sanda da ke yankin Surulere, amma ba a samu Amaha ba, domin wayarta ya na kashe, sannan wurin da ce ta na zaune da kuma wanda ya tsaya mata na duk na karya ne.

Matar mai suna Misis Taiye ta bayyana cewa, ta sanar wa Sufeton ‘yan sanda na kasa Mohammed Adamu tare da mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari, faruwar lamarin, inda su ka kaddamar da farautar ‘yar aikin.

Daga baya tawagar ‘yan sandar Jihar Legas, sun samu nasarar damke Amaha, a gidan kawarta da ke yankin Ajah cikin Jihar Legas.

Lokacin a ka yi hira da Amaha, sai ta bayyana cewa, ta sace wannan kudi ne domin ta yi jinyar mahaifiyarta wacce ta ba da lafiya.  Ta kara da cewa, “na zo Legas a shekarar 2014, inda na fara aiki da wata mata mai suna Misis Tina Okiro. Bayan da na shafe shekaru biyu da rabi da matar, sai ta fara min korafi a kaina, da na ji korafin ya yi yawa, sai na bar mata gidanta, inda na koma kan titi ina karuwanci. Lokacin da dan’uwana ya ji abinda na ke yi, sai ya kira ni a kan indawo gida, sai na koma kauye na kwashe wasu lokuta tare da dan’uwana a garin Onitsha. Na kara dawowa Legas, inda na yi aikin gida a wurin wata mata da ke yankin Ikorodu na tsawon wata uku kafin in koma kauye in cigaba da yin noma. Na kara dawowa Legas domin in samu kudi, na samu wani mutum mai suna Frank wanda shi ne ya nada ni da Mista Ade, inda ita kuma ta hada ni da wata mata a Surulere. Kafin in fara aiki a gidan, matar ta bayyana min dukkan irin aikin da zan yi mata har da albashin da za ta tunga ba ni a wata.

Na ba ta mazauni na karya da kuma wanda ya tsaya min duka na karya na ba ta, domin ina da niyyar yin sata a gidan. Na fara aiki a gidan matar da misalin karfe 12 na rana, ta tura ni filin jirjin sama da misalin karfe 3.30 na rana, domin na dauko ‘yar’uwarta. Na fude jakar ‘yar’uwar matar, sannan na sace mata dala 700 da kuma fam 100. Na canza dala 100, inda ya gyara kaina sai na sayi salifas, sannan sauran kuma na saka su a asusuna na banki,” in ji ta.

Exit mobile version