Daga Muhammad Shafi’u, Yola
Wata ’yar jarida daga arewa maso gabashin Najeriya ce ta lashe lambar yabo ta BBC ta Komla Dumor ta bana.
Amina Yuguda mai gabatar da labarai ce a gidan talbijin na Gotel da ke Yola, inda ta gabatar da labarai da dama har da wadanda suka shafi rikicin Boko Haram.
Za ta fara aikin koyon sanin makamar aiki na tsawon wata uku a Landon cikin watan Satumbar 2017.
Amina Yuguda ta ce samun nasararta ‘babbar girmamawa ce.”Farin ciki ya lullube ni. Masu bayar da labari ko da yaushe suna da muhimmiyar rawar takawa a Afirka… wannan ne abin da yake fito da mu. A yau ’yan jarida na daukar wannan nauyin.”
Ta burge tawagar tantancewar saboda yadda ta nuna shauki kan yadda makiyaya ke amfani da rediyo a yankinta, kamar yadda ta fada a takardarta ta neman shiga gasar:
“Duk da rashin ilimi ko karancin ilimi, mutanen kasata sun san abubuwa da yawa kan al’amura da dama da suka hada da shugabancin Trump a Amurka, da rashin tsoron Koriya Ta Arewa, da dangantakar Rasha da kasashen waje karkashin mulkin Putin da dai sauran su.”
Daraktar kafar yada labarai ta BBC Francesca Unsworth ta ce Amina Yuguda ta cancanci samun nasara: “Samun wani wanda ya hada irin halayyar Komla ta fannin aiki wani abu ne da ya kamata mu yi murnarsa, kuma mun yi matukar jin dadin yin aiki da Amina.”
Wadanda suka samu nasarar cin wannan gasa ta Komla a baya dai sun hada da mai gabatar da labarai ‘yar Uganda Nancy Kacungira, da kuma kuma ’yar jaridar Nijeriya da ta kware a labaran kasuwanci, Didi Akinyelure.