Mahdi M Muhammad" />

’Yar Mai Gida Ta Kashe Dan Haya Kan Kudin Lantarki

Takaddama kan kudin wutar lantarki da ta barke tsakanin ‘yar wata mai gida, Tina Essi, da mai haya, ya yi sanadiyyar mutuwar dan haya a yankin Ikorodu da ke jihar Legas.

Har zuwa lokacin da lamarin ya faru, dukkansu mazauna gida daya ne a No 26 Orijamogun Street, Oreyo, Ikorodu, Legas
Bugu da kari, Tina a yanzu haka tana hannun sashen binciken manyan laifuka na jihar da ke Panti, Yaba, Legas.
Da ya ke ba da cikakken bayani game da kamun Tina, Kakakin rundunar, CSP Ademuyiwa Adejobi ya bayyana cewa, binciken farko da ‘yan sanda suka gudanar ya nuna cewa a ranar 31 ga Janairun 2021, takaddama kan biyan kudin wutar lantarki ya shiga tsakanin su biyun wanda ya haifar da fada. Bayan fadan, marigayin ya ci gaba da fama da tsananin ciwon ciki wanda hakan yasa a ranar Asabar 6 ga Fabrairu 2021 da misalin karfe 7 na safe aka garzaya da shi zuwa babban asibitin Ikorodu, wanda a can ya cika.
An tuntubi jami’an ‘yan sanda da ke sashin Ikorodu na rundunar tare da cafke wacce ake zargin nan take. Kwamishinan ‘yan sanda ya ba da umarnin a tura wacce ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar, SCIID, Panti don gudanar da cikakken bincike.
Kakakin ya ce, kwamishinan ‘yan sanda, kwamandan rundunar ta jihar Legas, CP Hakeem Odumosu ya roki dangin mamacin da su kwantar da hankulansu domin rundunar za ta yi abin da ya dace don ganin an yi adalci a lamarin.
Shugaban ‘yan sandan ya kuma yi kira ga ‘yan Legas da su kasance masu kula da bambance-bambancensu da rikice-rikicen da suke yi, wanda duk lokacin da hakan ya faruwa ya kamata su nemi ‘yan sanda su shiga tsakani a inda ya dace don kauce wa mutuwar bazata da shiga cikin matsaloli.

Exit mobile version