Yar Shekara 14 Ta Zama Gwamnan Bauchi Na

‘Daga Khalid Idris Doya,

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad ya dauki matakin mika kujerar ikonsa ga wata ‘yar asalin jihar mai shekaru goma sha hudu a duniya Aisha Katagum.

Aisha ta samu wannan babban damar ce a lokacin da gwamnan ya yi kokarin nuna wa yara mata yadda ake gudanar da mulki da shugabanci a matsayinsu na manyan gobe.

A cikin bikin murnar zagayowar ranar ‘ya mace ta duniya na wannan shekara, gwamna Bala Muhammad ya sauka daga kujerar sa tare da dora Aisha Katagum, wacce ta gudanar da lamuran mulki duk cikin bikin na wannan shekara.

Da yake jawabinsa gwamna Bala, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su marawa shirin inganta ilimin ‘yaya mata baya, inda ya taya al’umma Murnar zagowar wannan ranar.

A cewar gwamnan gwamnatinsa ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen samar da kayan inganta rayuwar al’umar jihar Bauchi musamman yara kanana shugabannin gobe.

Ya ce tuni gwamnatinsa ta gyara daruruwan dakunan karatu a makarantu da dama a fadin jihar kuma za ta cigaba da samar da sabbi don yaki da jahilci.

Ya bayyana cewar kula da tarbiyyar ‘ya mace ya dauru ne a kan dukkanin al’umma musamman iyaye, sai ya jawo hankalinsu da su Kara kokari wajen kula da rayuwar ‘ya’ya Mata domin rayuwarsu ta inganta tare da dakile cin zarafin mata.

Exit mobile version