Daga Abdullahi Muhammad Sheka,
Wata budurwa mai shekaru 28 a duniya, ta samu nasarar bude wurin koyar da sana’o’i iri daban- daban ga mata ‘ya’uwanta, inda a cikin shekara guda ta yaye masu koyon sana’ar zanen gado, dardumar daki, kayan kawata daki da kuma kayan kamshi. Hakan ya sanya manya-manyan mutane matukar mamakin gaske, ganin yadda wannan yarinya ta samu karfin halin yin wannan gagarumin aikin alhairi.
Malama Rafi’atu Muhammad Jibrin, haifaffiyar Unguwar Kawon Maigari ce da ke yankin Karamar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano, an haife ta a shekarar 1993, ta kuma yi karatun Firamarenta da na Karamar Sakandire duk a Karamar Hukumar ta Nasarawa. Daga nan kuma aka tafi da ita zuwa Jihar Zamfara, inda ta karasa Babbar Sakandirenta ta kuma samu sukunin shiga Makarantar Horar da ilimi mai zurfi tare da samun shaidar diploma.
Bayan dawowarta gida Kano ne kuma, sai ta kara fadada tunaninta a kan yadda za ta taimakawa al’ummar da ta fito daga cikinsu, musamman ganin tun tana karama ta iya sana’ar jakunkuna, zanen gado da sauran kayan kawata daki, wanda ta ce jama’ar Unguwar ta Kawon Maigari duk a wurin ta suke sayen ire-iren wadannan kayayyaki.
Rafi’atu Muhammad Jibrin, ganin cewa ita mace ce wanda ke da burin yin aure nan ba da jimawa ba, ta fahimci idan har ta tafi gidan miji ba dole ne a wannan Unguwa za ta zauna da mijinta ba, kenan kwastomominta ba za su ci-gaba da samun wadannan kayayyaki ba, hakan tasa ta yanke shawarar bude wannan Cibiya wadda a halin yanzu akwai mata sama da 50 da suke koyon wadannan sana’o’i, sannan kuma zuwa yanzu har an yaye guda 30 wadanda suka kammala koyon sana’o’in daban-daban, wanda ta ce ba ta shakkar duk inda suka shiga za su ci-gaba da aiwatar da wadannan sana’o’i da suka koya a wajenta.
Da ta ke yin tsokaci akan abinda gwamnati da sauran masu rike da mukaman siyasa ya kamata su yi, cewa ta yi, “Idan da a ce za su hada kai da mu su ci-gaba da kawo mana muna koya masu wadannan sana’o’i, nan ba da jimawa ba za a samu saukin mace-macen aure, sannan kuma jama’a za su zama masu dogaro da kawunansu.
Ta kara da cewa, a shirye muke idan gwamnati za ta shigo ta tallafa mana da kayan aiki irin na zamani da wurin koyar da wadannan sana’o’i wadatacce, tunda yanzu a shagon gidanmu nake koyawa matan wadannan ayyuka.
A karshe, ta gode wa Alhaji Nasiru Baba Nabegu bisa damuwar da ya nuna da kuma kaunar ci-gaban wannan Cibiya. Sannan ta roki Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Dakta Nasiru Yusif Gawuna kasancewar sa dan asalin wannan Karamar Hukuma, da ya shigo cikin wannan aikin alhairi, domin taimakawa rayuwar mata a wannan jiha tamu mai albarka.